An Ja Daga Tsakanin Amurka da China kan Haraji, Kasar Ta Gargadi Trump

An Ja Daga Tsakanin Amurka da China kan Haraji, Kasar Ta Gargadi Trump

  • Kasar China ta soki sababbin harajin da Amurka ta ƙaƙaba kan kayayyakinta da na wasu ƙasashe 59
  • Amurka ta ce harajin ya danganci hana shigo da kayayyakin da ake zargin an samar da su ta hanyar aikin dole
  • Beijing ta ce za ta ci gaba da aiki da Amurka wajen rage takaddamar haraji, amma matakan na iya sake jawo da matsala

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Beijing, China - Kasar China ta yi Allah wadai da sababbin harajin da Amurka ta ƙaƙaba kan kayayyakin da ake shigowa da su daga China.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa matakin ya shafi kasar da wasu ƙasashe 59 bisa zargin amfani da aikin dole.

China ta gargadi Amurka kan kakaba haraji
Shugaba Xi Jinping na China na gaisawa da shugaban Amurka, Donald Trump Hoto: Kenny Holston.
Source: Getty Images

Mai magana da yawun Ma'aikatar Harkokin Wajen China, Lin Jian, ya bayyana wa manema labarai cewa ƙasarsa tana adawa da duk wani nau'in haraji na bai ɗaya, cewar rahoton CNA.

Kara karanta wannan

Trump ya kara tsaurara matakan kasuwanci, ya laftawa Najeriya haraji

Korafin da China ke yi ga Amurka

Beijing ta bayyana cewa ba ta amince da duk wani matakin haraji da ƙasa guda ke ɗauka ita kaɗai ba, tana mai gargadin Amurka kada ta sake jawo matsala a bangaren kasuwanci.

Sababbin harajin da Amurka ta sanar sun kai tsakanin kashi 10 zuwa 12.5 cikin ɗari, yayin da China ta fuskanci mafi girman harajin cikin jerin ƙasashen.

Ya ce matsalar haraji da yaƙin kasuwanci ba su da amfani ga kowace ƙasa, yana mai jaddada cewa irin waɗannan matakai na iya lalata dangantakar tattalin arziki.

Sababbin harajin sun maye gurbin wani harajin duniya da Shugaban Amurka Donald Trump ya ƙaddamar a farkon wannan shekara, wanda wa'adinsa ya ƙare.

Trump ya kakaba haraji ga kasashe da dama
Shugaba Donald Trump yayin taron karbar gawar daya daga cikin sojojin da suka mutu a yaƙi Iran. Hoto: Kevin Dietsch.
Source: Getty Images

Gwamnatin Trump ta kawo sababbin matakai kan haraji

Gwamnatin Trump ta gaggauta sake ƙarfafa manufofinta na haraji bayan Kotun Koli ta Amurka ta soke wasu daga cikin harajin da shugaban ya ƙaƙaba a watan Fabrairun 2026, cewar Vanguard.

Jami'in kasuwancin Amurka, Jamieson Greer, ya ce Washington na aiwatar da dokar hana shigo da kayayyakin da aka samar ta hanyar aikin dole ba tare da sassauci ba.

Kara karanta wannan

Idon Trump ya koma kan kadarorin Iran da ke Amurka, ya fara kai masu barazana

Ya kuma ce lokaci ya yi da sauran ƙasashen duniya za su ɗauki irin waɗannan matakai domin dakile cin zarafin ma'aikata da kare haƙƙin ɗan Adam.

Ƙasashe irin su Canada, Tarayyar Turai da Birtaniya, waɗanda suka haramta kayayyakin aikin dole, sun samu mafi ƙarancin harajin kashi 10 cikin ɗari.

Sai dai manyan abokan kasuwancin Amurka kamar India da Japan sun fuskanci harajin kashi 12.5 cikin ɗari saboda sabon tsarin da aka sanar.

China da Amurka sun shafe babban ɓangaren shekarar da ta gabata suna takun saƙa kan batun haraji kafin shugabanninsu Donald Trump da Xi Jinping su cimma sulhu.

Bayan ziyarar da Trump ya kai Beijing a wannan shekara, China ta ce za ta yi aiki tare da Amurka wajen rage haraji, amma sabbin matakan na iya sake tayar da rikicin kasuwanci.

Trump zai kai hari a Mali

A wani labarin, an ji cewa shugaban kasar Amurka, Donald Trump na nazarin ƙaddamar da hare-haren soji kan wata ƙungiya mai alaƙa da al-Qaeda a ƙasar Mali.

İdan har aka amince da harin, Mali za ta zama ƙasa ta takwas da Amurka za ta kai wa hari tun bayan dawowar Trump kan mulki karo na biyu.

Gwamnatin tana nazarin kai harin ne kan ƙungiyar JNIM, wadda ta amsa alhakin ƙaddamar da hare-hare da sace-sacen mutane a Afirka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.