Cikin Sauki, An Fadawa Kasaahen Turai Hanya 1 da Za Su Sulhunta Amurka da Iran
- Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian ya tattauna da Shugaban Faransa, Emmanuel Macron ta wayar tarho ranar Litinin
- Pezeshkian ya fadawa Macron cewa akwai bukatar Turai ta sa baki don Amurka ta bi dokokin kasa da kasa a tattaunawar sulhu
- Ya jaddada cewa barazana ko daukar matakin soji ba za su kawo karshen matsalar da ta jawo barkewar yaki tsakanin kasashen ba
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Iran - Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya yi wata tattaunawa mai matukar muhimmanci da takwaransa na kasar Faransa, Emmanuel Macron kan halin da ake ciki.
Shugaba Pezeshkian ya tabo batun yadda za a kawo karshen yakin kasar Iran da Amurka yayin wannan tattaunawa da ya yi Macron ta wayar tarho yau Litinin, 13 ga watan Afrilu, 2026.

Source: Getty Images
Shugaban Iran ya yi waya da Macron
A hirar da suka yi ta wayar tarho kamar yadda tashar Al-Jazeera ta wallafa, Shugaban Iran ya bukaci kasashen Turai su shiga tattaunar sulhu da aka fara tsakanin Iran da Amurka.
A cewarsa, akwai bukatar kungiyar Tarayyar Turai ta sa baki kuma ta taka muhimmiyar rawa wajen kawo karshen wannan yaki na Gabas ta Tsakiya.
Iran ta yi zama da tawagar Amurka
Wannan kira da Shugaba Pezeshkian ya yi na zuwa ne awanni 24 kacal bayan zaman farko da aka yi a birnin Islamabadan tsakanin Iran da Amurka ya kare ba tare da cimma matsaya ba.
Tuni dai Pakistan ta ci gaba da kokarin shawo kan bangarorin biyu domin su koma teburin tattaunawa, kuma ana sa ran za ta cimma nasara kafin cikar wa'adin tsagaita wuta.
Iran da Amurka/Isra'ila sun dakatar da kai wa juna hare-hare ne bayan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta makonni biyu a ranar Talata da ta gabata.
A wani sako da ya fitar yau Litinin, Pezeshkian ya jaddada kudirin Tehran na ci gaba da tattaunawa da Amurka amma bisa bin tsarin dokokin kasa da kasa.

Kara karanta wannan
Wata sabuwa: Matsalar da aka samu a sulhun Amurka da Iran ya rusa burin 'yan Najeriya
Abin da ya kamata kasashen Turai su yi
Shugaban na kasar Musulunci ya kara sa cewa duk wata hanya da ta saba wa ka’idojin kasa da kasa na zama cikas ga cimma yarjejeniya mai dorewa.
Pezeshkian ya fada wa Macron ta wayar tarho cewa:
“Turai na iya taka muhimmiyar rawa wajen karfafa Amurka ta bi wadannan ka’idoji.
Ya kuma kara da cewa hanyoyin da suka hada da barazana, matsin lamba da amfani da karfin soja ba za su warware matsalar ba, illa ma za su kara dagula al’amura da kuma tsananta matsalolin da Amurka ta janyo da kanta.

Source: Getty Images
Shugaban na Iran ya jaddada cewa bin dokokin kasa da kasa ne kadai zai samar da mafita mai dorewa ga rikicin da ke gudana tsakanin bangarorin biyu, cewar tahoton Vanguard.
Birtaniya ta juya wa Amurka baya
A baya, kun ji cewa Firaminista Keir Starmer ya sanar da cewa Birtaniya ba za ta sa hannu wajen toshe tashoshin jiragen ruwan Iran ba.

Kara karanta wannan
Muhimman abubuwa 5 da Amurka da Iran suka gaza warwarewa a zaman sulhu a Islamabad
Starmer ya bayyana cewa babban burinsa shi ne ganin an buɗe mashigar ruwa ta Hormuz baki ɗaya domin rage farashin makamashi cikin gaggawa.
Keir Starmer ya kauce wa yin sharhi kan ayyukan soji na musamman, yana mai nanata cewa Birtaniya ba ta goyon bayan matakin killace ƙasar Iran.
Asali: Legit.ng
