China Ta Shigarwa Iran Fada da Amurka kan Toshe Mashigar Hormuz
- A wani mataki mai ƙarfi na diflomasiyya, kasar China ta sake jaddada goyon bayanta ga Iran yayin da tashin hankali ke ƙaruwa a mashigar ruwan Hormuz
- Ministan tsaron China ya ce Beijing na sa ido sosai kan halin da ake ciki, yana mai jaddada aniyarta ta tabbatar da zaman lafiya Gabas ta Tsakiya
- China ta nuna cewa jiragen ruwan ta na ci gaba da zirga-zirga cikin ‘yanci a muhimmiyar mashigar da ke jigilar kaso mai yawa na makamashi a duniya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Iran - China ta nuna goyon bayanta ga Iran tare da gargadi kan tsoma baki, bayan da Amurka ta sanar da kulle hanyoyin ruwa da ke shafar zirga-zirgar jiragen ruwa ta mashigar Hormuz.
Da yake mayar da martani, Ministan tsaron China ya ce ƙasarsa na da kudurin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya.

Source: Getty Images
Rahoton Economics Times ya nuna cewa kasar China ta ce za ta cigaba da saka ido ga dukkan abubuwan da suke faruwa a hanyoyin ruwan.
Gargadin Gwamnatin China ga Amurka
China ta bayyana goyon bayanta ga Iran tare da gargadin Amurka da kada ta tsoma baki a harkokinta, bayan tashin hankalin da ya biyo bayan kulle mashigin ruwan Hormuz.
Ma’aikatar harkokin wajen China ta ce ƙasarta na goyon bayan Iran wajen kare ikon ƙasarta da kuma muradunta, tana mai jaddada cewa kowace ƙasa na da ‘yancin kare kanta daga abin da ta kira matsin lamba daga waje.
Ta kuma yi kira ga Amurka da ta guji tsoma baki cikin al’amuran cikin gida na China ko na Iran, tana mai cewa irin wannan mataki na iya ƙara tayar da hankali a yankin da ma duniya baki ɗaya.
Matakin Amurka a kan Hormuz
Yayin barazanar toshe hanyar, Donald Trump ya bayyana cewa rundunar Amurka ba za ta hana ‘yancin zirga-zirga ga jiragen ruwa da ke wucewa ta mashigar Hormuz zuwa da daga tashoshin da ba na Iran ba.
Business Today ta rahoto cewa Amurka ta sanar da cewa za a ba da ƙarin bayani ga masu jiragen ruwa na kasuwanci ta hanyar sanarwar hukuma kafin fara aiwatar da kullen.

Source: Getty Images
Ta kuma shawarci duk masu jiragen ruwa da su rika sauraron sanarwar da za a fitar tare da tuntuɓar rundunar ruwa ta Amurka ta hanyar tashar sadarwa da ke aiki a Tekun Oman da hanyoyin shiga Hormuz.
Matakin Amurka ya biyo bayan gaza cimma matsaya a tattaunawar tsagaita wuta tsakanin Washington da Tehran a Pakistan bayan yakin da suka yi.
Sojojin Uganda za su farmaki Iran
A wani rahoton, kun ji cewa babban sojan kasar Uganda ya yi barazanar kai farmaki Iran domin taya Isra'ila yaki yayin da aka tsagaita wuta.
Janar Muhoozi Kainerugaba ya sanar da cewa a shirye ya ke da ya tura sojoji 500,000 su kwace Tehran, babban birnin kasar Iran.
Ya kuma bayyana cewa Uganda za ta iya tura sojoji 100,000 domin kare Isra'ila daga barazanar da za ta iya fuskanta daga kowace kasa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

