Kasar Iran Ta Jero Sunayen Kasashe 5 da Take Bukatar Su Biya Ta Diyya kan Yakin Amurka
- Kasar Iran ta sake jaddada bukatarta ta neman diyyar barnar da aka mata a yakin da ya gudana tsakaninta da Amurka da Isra'ila
- Wakilin Iran a Majalisar dinkin duniya, Amir Saeid Iravani ya jero sunayen kasashen da kasarsa ke son ta biya diyyar barnar yaki
- Ya ce suna zargin kasashen sun taimaka wa Amurka da Isra'ila wajen kai wa Iran hare-hare a yakin da ya shafe sama da wata guda
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Iran - Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta fara bayyana kasashen da take bukatar su biya ta diyyar barnar da aka mata a yakin da kasar ta yi da kasashen Amurka da Isra'ila.
Tun farko dai batun biyan diyya na daya daga cikin sharuddan da Iran ta gabatar a yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma wa a makon jiya.

Source: Getty Images
A rahoton da NBC News ta kawo, an ce Iran ta bayyana cewa za ta bukaci wasu kasashen yankin Gulf su biya ta diyya saboda zargin da take masu na taimaka wa abokan gabarta.
Iran ta fadi kasashen da za su biya diyya
Jakadan din din-din na Iran a Majalisar Dinkin Duniya, Amir Saed Iravani ne ya bayyana hakan, yana mai cewa kasar na neman diyya daga kasashen yankin Gabas ta Tsakiya.
Ya ce za su nemi diyyar ne sakamakon rawar da ake zarginsu da takawa a yakin da Amurka da Isra’ila suka kaddamar a kanta, wanda ya shafe fiye da wata guda.
Kamfanin dillancin labarai na Tasnim, wanda ke da alaka da rundunar sojojin juyin juya hali (IRGC) ta Iran, ya ruwaito sunayen kasashen wakilin da wakilin Iran ya ambata.
Iravani ya ce Iran na neman diyya daga kasashen Bahrain, Saudiyya, Qatar, Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma Jordan.

Kara karanta wannan
Muhimman abubuwa 5 da Amurka da Iran suka gaza warwarewa a zaman sulhu a Islamabad
Dalilin Iran na neman diyya daga kasashe 5
A cewarsa, Iran na ganin wadannan kasashe sun taka rawa a hare-haren da Amurka da Isra’ila suka rika kai mata, duk da cewa bai bayyana takamaiman irin taimakon da kowace kasa ta ba abokan gabarta ba.
Rahoton ya nuna cewa ba a fayyace yadda wadannan kasashe suka shiga yakin ba, sai dai an san cewa Amurka na da sansanonin soja a wasu daga cikinsu, wanda hakan na iya zama daya daga cikin dalilan da Iran ke jingina zargin.
Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da rikicin yankin ke kara tsananta, inda ake ci gaba da samun takaddama tsakanin Iran da kasashen yamma da kawayensu duk da cewa an tsagaita wuta.

Source: Getty Images
Masu sharhi na ganin cewa wannan bukata ta diyya na iya kara dagula alakar diflomasiyya tsakanin Iran da kasashen yankin, musamman idan ba a samu fahimtar juna ba.
Har zuwa yanzu, babu wata sanarwa daga kasashen da aka ambata dangane da wannan zargi ko kuma bukatar diyya da Iran ta gabatar, kamar yadda Al-Jazeera ta ruwaito.
Shugaban Iran ya yi waya da Macron
A wani rahoton, kun ji cewa Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian ya tattauna da Shugaban Faransa, Emmanuel Macron ta wayar tarho ranar Litinin, 13 ga Afrilun 2026.
Shugaban Iran ya bukaci kasashen Turai su shiga tattaunar sulhu da aka fara tsakanin Iran da Amurka domin tabbatar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya.
Pezeshkian ya jaddada kudirin Tehran na ci gaba da tattaunawa da Amurka amma bisa bin tsarin dokokin kasa da kasa, yana mai cewa haka ne kadai hanyar warware rikicin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

