'Iran Ke Haddasa Rikici a Gabas ta Tsakiya': Kasashe 7 Sun Goyi bayan Isra'ila

'Iran Ke Haddasa Rikici a Gabas ta Tsakiya': Kasashe 7 Sun Goyi bayan Isra'ila

  • Shugabannin kasashen G-7 sun goyi bayan Isra'ila, yayin da suka kira Iran da zama tushen duk wani rikici da ke faruwa a Gabas ta Tsakiya
  • Kungiyar G-7 ta jaddada haƙƙin Isra'ila na kare kanta, tana mai cewa ba za ta amince Iran ta taɓa mallakar makamin nukiliya ba
  • Iran da Isra'ila sun amince da tsagaita wuta bayan kwanaki 12 na musayar hare-hare, biyo bayan shawarar Shugaba Donald Trump

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Canada - Ƙungiyar ƙasashe bakwai masu ƙarfi wato G-7, ta bayyana goyon bayanta ga Isra’ila a wata sanarwa da ta fitar bayan taronta a Kananaskis, Albertaa.

Shugabannin G-7 sun bayyana Iran a matsayin tushen rikici da rashin zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya yayin da suka nemi a kawo karshen rikice-rikice a yankin.

Shugabannin kasashen G-7 sun goyi bayan Isra'ila na hare-haren kare kai da ta kai Iran
Shugabannin manyan kasashen duniya 7 a taron da suka yi a Kananaskis, kasar Canada. Hoto: Chip Somodevilla / Staff
Asali: Getty Images

Kasashen G-7 sun goyi bayan Isra'ila kan Iran

Yaƙin kwanaki 12 da aka yi tsakanin Iran da Isra’ila ya kara tayar da hankula a yankin da tuni ya shiga rikici tun bayan barkewar hare-haren Isra’ila kan Gaza a watan Oktoban 2023, inji rahoton Reuters.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugabannin G7 sun ce:

“Muna tabbatar maku da cewa Isra’ila na da haƙƙin kare kanta. Kuma muna kara jaddada goyon bayanmu ga tsaron Isra’ila.”

Yayin da shugabannin kasashen duniyar bakwai suka nanata cewa ba su yarda Iran ta mallaki makamin nukiliya ba, sun kuma ce:

“Iran ita ce babban tushen rashin zaman lafiya da ta’addanci a yankin Gabas ta Tsakiya."

Yakin Iran-Isra'ila kan mallakar nukiliya

Legit Hausa ta rahoto cewa Isra’ila ta kai harin farko kan Iran a ranar Juma’a, 13 ga watan Yuni, inda ta ce matakin na rigakafi ne don hana Tehran samun makaman nukiliya.

Tun daga lokacin, ƙasashen biyu suka ci gaba da kai wa juna farmaki, inda jami’an Iran suka ce sama da mutane 500 ne suka mutu, mafi yawansu fararen hula, yayin da Isra’ila ta ce sama da mutane 50 ne suka mutu, su ma fararen hula.

Kasashen G-7 sun tabbatar da cewa ba za su taba goyon bayan Iran ta mallaki nukiliya ba
Shugabannin manyan kasashen duniya 7 a taron da suka yi a Kananaskis, kasar Canada. Hoto: Chip Somodevilla / Staff
Asali: Getty Images

Iran ta musanta zargin cewa tana ƙoƙarin kera makamin nukiliya, tana mai cewa tana da ‘yancin raya fasahar nukiliya domin dalilai na lumana.

A cewar rahoton India Today, Iran ta ce raya fasahar nukiliya ya hada har da tace sinadarin Uranium, a matsayin mamba a yarjejeniyar hana yaɗuwar makaman nukiliya (NPT).

Isra’ila kuwa, ta ki shiga wannan yarjejeniya ta NPT, kuma ita ce kadai ƙasa a Gabas ta Tsakiya da ake zargi da mallakar makaman nukiliya. Duk cewa ba ta tabbatar da hakan ba, amma ba ta musanta ba.

Yarjejeniyar tsagaita wuta bayan kwana 12

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Iran da Isra'ila sun amince da tsagaita wuta bayan kwanaki 12 na musayar hare-hare masu zafi ta sama.

Firayim Minista Benjamin Netanyahu ya bayyana cewa Isra'ila ta amince da shawarar tsagaita wutar da Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar.

Sanarwar Isra'ila ta fito ba da jimawa ba bayan da Trump ya bayyana cewa tsagaita wutar ta fara aiki kuma ya roƙi ƙasashen biyu da "kada su karya ta."

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.