Fargabar Yakin Duniya: An Gano Kasashe 5 Masu Kera Makaman Nukiliya a Sirrance

Fargabar Yakin Duniya: An Gano Kasashe 5 Masu Kera Makaman Nukiliya a Sirrance

  • Tashe-tashen hankula a duniya sun karu, tare da fargabar durkushewar yarjejeniyar gwajin nukiliya da kuma yiwuwar barkewar yakin duniya
  • Yawan makaman nukiliya a duniya da ake kerawa a sirrance ya karu sosai, inda kasashe biyar suka kara sama da makamai 700 a ma'ajiyarsu
  • Kungiyar masana kimiyya na Amurka ta yi gargadin cewa akwai karin kasashe da ke kera makaman nukiliya har yanzu, kuma hakan barazana ce

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

A yayin da duniya ke ci gaba da fuskantar ƙarin matsin lamba daga manyan ƙasashe masu ƙarfi, batun Yaƙin Duniya na Uku yana ci gaba da zama abin damuwa ga mutane.

Kasashe da dama na kara yawan makaman nukiliyarsu a boye domin kare kansu ko kuma kasancewa cikin shirin barkewar yaƙin duniyar na gaba.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kutsa cikin gida a Kano, sun yi ta'asa bayan cirewa wani ƴan yatsu

Rahoton FAS ya nuna cewa kasashe 5 suna kera makaman nukiya a sirrance
Kasashe na kara yawan makaman nukiliyarsu saboda fargabar yakin duniya na 3. Hoto: Dzymity Dzemidovich via Getty Images
Asali: Getty Images

Rahoton Daily Mail ya nuna cewa cibiyar binciken zaman lafiya ta kasa da kasa (SIPRI) da cibiyar masana kimiyar tarayyar Amurka (FAS) sun gano cewa akwai ƙasashe biyar da ke ƙara adadin makaman nukiliyarsu ba tare da sanin duniya ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kasashe 5 masu kara yawan nukiliya a sirrance

Ga cikakken bayani game da waɗannan ƙasashe da yadda suke ƙara ƙarfinsu na nukiliya.

1. China: Ƙarfin nukiliyarta na ƙaruwa fiye da ƙima

Kasar China tana daga cikin ƙasashen da ke ƙara yawan makaman nukiliyarsu cikin sirri.

A cewar rahoton Financial Times, kasar tana da makaman nukiliya 410 a shekarar 2023, kuma ana tsammanin wannan adadi ya haura 500 a 2025.

Masana harkokin tsaro sun bayyana cewa China na kokarin samar da makaman nukiliya masu ƙarfi don yin gasa da Amurka da Rasha a fannin tsaron duniya.

Rahoton ya ce a 2023, Pentagon yi ikirarin cewa China na iya ninka yawan makaman nukiliyarta zuwa 1,500 nan da shekara ta 2035.

Kara karanta wannan

Da gaske ne Atiku ya sauya sheka, zai yi takarar 2027 a SDP?

Ƙasar tana ƙara yawan wuraren ajiyar makaman nukiliyarta a yankin Xinjiang, inda take gina sama da sababbin ramukan kaddamar da gwajin makaman nukiliya 300.

Wannan yana nuni da cewa kasar na iya zama babbar barazana idan har Yaƙin Duniya na Uku ya barke, kuma a wajenta, wannan shiri ne na ko-ta-kwana.

A cikin watan Janairu 2024, gwamnatin China ta bayyana cewa ba za ta taɓa amfani da makaman nukiliya don kai harin farko ba, amma masana harkokin tsaro na ganin hakan na iya sauyawa.

2. Rasha: Jagorar Duniya a fannin makaman nukiliya

Rasha ita ce ƙasa mafi yawan makaman nukiliya a duniya. A cewar rahoton FAS, kasar na da sama da makaman nukiliya 5,889, wanda ke nufin ta zarce Amurka a wannan fanni.

Tun bayan barkewar yaƙin Ukraine a 2022, Rasha ta ƙara kokarin haɓaka ƙarfin nukiliyarta.

Shugaba Vladimir Putin ya bayyana cewa ƙasarsa za ta kara yawan makaman da ake kera wa, musamman na hypersonic nuclear, inji jaridar Huff Post.

Kara karanta wannan

Me ke faruwa da PDP? An rufe siyar da fom na takarar gwamna, babu wanda ya siya

Rahoton ma'aikatar tsaron Rasha ya nuna cewa kasar tana gwaje-gwajen sababbin makaman nukiliya masu sauri fiye da ƙarar iska, irin su nukiliyar Avangard hypersonic, wanda ke iya kai hari a kowane yanki na duniya cikin sa'o’i kaɗan.

Kazalika, ƙasar ta ƙaddamar da sabbin jilaragen ruwa masu ɗauke da makaman nukiliya a Tekun Arctic, inda take son kafa kariya daga Amurka da NATO.

Kasashe 5 na kera makaman nukiliya a sirrance
Dakin kula da harkokin makaman nukiliya a sansanin makamai da ke wajen birnin Moscow. Hoto: robert wallis/Corbis via Getty Images
Asali: Getty Images

3. Amurka: Haɓaka sababbin makaman nukiliya

Amurka na da sama da makaman nukiliya 5,244, kuma tana ci gaba da sabunta su don tabbatar da kariyar ƙasarta da abokan hulɗarta.

A cewar hukumar tsaron Amurka, gwamnatin Amurka ta ware sama da dala biliyan 750 domin sabunta shirinta na nukiliya daga yanzu har zuwa shekarar 2030.

A watan Janairu 2024, Shugaba Joe Biden ya amince da shirin ƙaddamar da sababbin makaman nukiliya na zamani kamar B61-12, wanda ke da ƙarfi fiye da duk wani makamin da Amurka ta taɓa mallaka.

Kara karanta wannan

Farashin man fetur ya kama hanyar ƙara araha, sauƙi zai lulluɓe ƴan Najeriya

Haka kuma, Amurka na ƙara ƙarfafa kawancenta da ƙasashen NATO, musamman a Turai da Asiya domin hana barazanar Rasha da China, inji rahoton FAS.

4. Indiya: Shirin kare kai daga abokan gaba

Indiya na daga cikin ƙasashen da ke ƙara yawan makaman nukiliyarsu ba tare da anji kansu ba.

A cewar wani rahoto na mujallar BAS, ƙasar tana da makaman nukiliya 170 a halin yanzu, amma tana shirin ƙara yawansu zuwa 200+ nan da 2030.

Tsohon Firaminista Manmohan Singh ya taba cewa Indiya na bukatar haɓaka ƙarfin nukiliyarta domin kare kanta daga abokan gaba kamar Pakistan da China.

A cikin shekarar 2023, gwamnatin Indiya ta kaddamar da sabbin makaman nukiliya irin su Agni-V, wanda ke iya kai hari a nisan 5,500km zuwa China da wasu yankuna masu mahimmanci.

Masana tsaro sun bayyana cewa Indiya na iya samun sababbin jiragen ruwa masu ɗauke da makaman nukiliya, wanda zai ƙara ƙarfin soja a yankin Asiya.

Kara karanta wannan

Obasanjo @ 88: Tinubu ya jinjina, ya jero alheran tsohon shugaban Najeriya

5. Koriya ta Arewa: Barazanar nukiliya ta kara tsananta

Koriya ta Arewa na daga cikin ƙasashen da ke ƙara yawan makaman nukiliyarta da kuma ci gaba da gwaje-gwajen sababbin makamai.

A cewar rahoton majalisar dinkin duniya na UNNR, ƙasar tana da sama da makaman nukiliya 50, amma ana zargin tana shirin haɓaka wannan adadi zuwa sama da 100 nan da 2030.

Shugaban ƙasar, Kim Jong Un, ya bayyana cewa ba wanda zai iya hana Koriya ta Arewa ƙarfafa shirinta na nukiliya, yana mai cewa hakan shi ne ginshikin tsaron ƙasar.

A cikin watan Maris 2024, ƙasar ta yi gwajin sabon makamin nukiliya mai suna Hwasong-18 ICBM, wanda ke iya kai hari a Amurka da Turai.

Haka kuma, gwamnatin Koriya ta Arewa ta bayyana cewa za ta ci gaba da gwaje-gwajen makaman nukiliyarta ba tare da jin tsoron NATO ko Amurka ba.

Rikicin Israila da Iran zai hargitsa Gabas ta Tsakiya

Kara karanta wannan

Kisan direbobi: Dattawan Arewa sun yi kaca-kaca da gwamnati da jami’an tsaro

A wani labarin, mun ruwaito cewa, tun bayan harin da Isra’ila ta kai ofishin jakadancin Iran a ranar Litinin, 1 ga Afrilu, jama’a suna ci gaba da tofa albarkacin baki kan abin da zai faru.

Wannan rikici ya haddasa fargaba, inda shugabanni da al’ummomi ke hasashen cewa yaki tsakanin kasashen biyu na iya haddasa gagarumin tashin hankali a Gabas ta Tsakiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.