Bayan Yaƙi da Iran, Isra'ila Ta Amince da Sharuddan Yarjejeniyar Tsagaita Wuta a Gaza
- Alamu sun nuna an kama hanyar kawo karshen kashe-kashen Falasɗinawa da Isra'ila ke yi a zirin Gaza na tsawon wata da watanni
- Shugaban Amurka, Donald Trump ya sanar da cewa Isra'ila ta amince da duka sharuɗɗan yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwanaki 60
- Ya yabawa ƙasashen Qatar da Masar da suka shiga tsakanin don kawo zaman lafiya, yana mai fatan Hamas ta amince da wannan yarjejeniya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
United States - Isra’ila ta amince da “sharuɗɗan" da aka shimfida domin cimma yarjejeniyar tsagaita wuta na tsawon kwanaki 60 a Gaza.
Shugaban Amurka, Donald Trump ne bayyana hakan ranar Talata, a wani ɓangare na ƙoƙarin kawo ƙarshen kisan kiyashin da ake yi wa Falasɗinawa.

Asali: Getty Images
A sanarwar da ya wallafa a shafin Truth Social na X, Shugaba Trump ya ce zai ci gaba da aiki da ɓangarorin biyu domin kawo ƙarshen wannan yaƙi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“A lokacin wannan yarjejeniyar tsagaita wuta da ake shirin cimmawa, za mu yi aiki tare da dukkan ɓangarori domin kawo ƙarshen yaƙin.”
Wane sharuɗɗa ne Isra'ila ta amince da su?
Sai dai Trump bai fayyace cikakkun sharuɗɗan da aka amince da su ba, amma ya yaba da rawar da Qatar da Masar suka taka a matsayinsu na masu shiga tsakani.
“Qatar da Masar, waɗanda suka yi namijin ƙoƙarin don dawo da zaman lafiya, su ne za su miƙa tayin ƙarshe, ina fatan Hamas za ta karɓi wannan yarjejeniya don abin ba zai fi haka sauƙi ba.
- Donald Trump.
Babu tabbaci har yanzu ko ƙungiyar Hamas ta Falasɗinawa za ta karɓi sharuɗɗan wannan tsagaita wutar.
Wannan yarjejeniya na zuwa ne kafin wata ganawa da Shugaba Trump ya shirya yi a mako mai zuwa da Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu.
An kashe Falasdinawa sama da 56,000
Isra’ila ta fara ƙaddamar da farmaki a Gaza ne bayan hare-haren da Hamas ta kai ranar 7 ga Oktoba 2023, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar akalla mutane 1,200.
Tun daga lokacin, akalla mutane 56,647 me suka mutu a Gaza sakamakon hare-haren Isra'ila, in ji ma’aikatar lafiyar yankin da Hamas ke jagoranta.

Asali: Getty Images
Da yake zantawa da BBC News, Jakadan Isra’ila a Majalisar Ɗinkin Duniya, Danny Danon, ya ce Isra’ila “na da niyyar tsagaita wuta”, amma ya zargi Hamas da ƙauracewa tattaunawa.
“Muna matsa wa Hamas lamba, kuma idan ba za su zauna da mu ba, zaɓi guda ne kawai zai rage mana don dawo da mutanenmu da suka riƙe, shi ne amfani da ƙarfin soja.
“Yaƙin zai ƙare ne idan aka dawo da mutanenmu gida," inji Danon.
A halin yanzu, kimanin ƴan Isra’ila 50 ne ke ci gaba da kasancewa a hannun Hamas a Gaza, inda aƙalla mutane 20 daga cikinsu ake tunanin har yanzu suna raye.
Trump ya yi ikirarin kare ran Khamenei
A wani labarin, kun ji cewa Shugaba Donald Trump ya yi ikirarin cewa shi ya hana kashe jagoran addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei.
Wannan kalamai na Trump na zuwa ne bayan shafe kwana 12 ana gwabza yaki tsakanin Isra'ila da Iran wanda ya jawo asarar rayukan ɗaruruwan mutane.
Shugaban Amurka ya zargi Khamenei da rashin godiya bayan ya ce harin da aka kai wa wuraren nukiliyarsu bai yi wata illa ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng