Trump Ya Magantu kan Sauya Gwamnatin Iran, Ya Faɗi Abin da Zai Tilasta Faruwar Haka
- Shugaba Donald Trump na Amurka ya tabo batun kifar da gwamnatin Iran kan wasu dalilai da ya kawo game da zama man teburin sulhu
- Trump ya fadi hakan ne musamman ganin idan gwamnatin Iran ta ki amincewa da tattaunawa kan shirin nukiliyarta
- Trump ya wallafa cewa me ya sa ba za a samu sauyin gwamnati ba a yanzu bayan jiragen Amurka sun kai hari kan wuraren nukiliyar Iran
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Washington DC, Amurka - Shugaban Amurka Donald Trump ya kuma tsoma baki kan rigimar da ke faruwa tsakanin Iran da Isra'ila.
Donald Trump yana ganin cewa ya kamata 'yan kasar Iran su kifar da gwamnatinsu idan ta ki amincewa da tattaunawa kan shirin nukiliyarta.

Asali: UGC
Trump yana bukatar zama a teburin sulhu
Sai dai, fadar White House ta bayyana cewa Trump har yanzu yana da sha’awar diflomasiyya, cewar rahoton BBC News.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wasu majiyoyi sun ce Trump yana bukatar Iran ta yarda da mafita ta lumana ba tare da zubar da jini ba.
Sakatariyar watsa labarai, Karoline Leavitt, ta ce:
“Idan gwamnatin Iran ta ki karbar mafita ta diflomasiyya, me ya sa jama’a ba za su dauke ikon ba?"
Trump ya tabo batun sauya mulkin Iran
A ranar Lahadi, jiragen yaki na Amurka sun kai farmaki kan wasu wuraren sarrafa makamashin nukiliya na Iran, suna goyon bayan yunkurin Isra’ila.
Rahotanni sun ce farmakin ya yi nasara kwarai, inda Trump ya ce:
“Mun yi mugun barna"
Iran tana fuskantar zargi daga Isra’ila da Amurka da wasu kasashen Yamma cewa tana kokarin kera makamin nukiliya, duk da musun gwamnatin Tehran.
A cikin rubutun da ya wallafa a ranar Lahadi, Trump ya ce:
"Ba daidai bane a siyasa a ce 'Canjin Mulki,' amma idan gwamnatin yanzu ta Iran ta kasa sake inganta Iran, me ya sa ba za a samu canjin mulki ba???"

Asali: Twitter
Maganar shugaba Trump ta jawo ka-ce-na-ce
Wannan maganar tasa ta saba da ra’ayin wasu daga cikin manyan abokan aikinsa, AP News ta ruwaito.
A karshen mako, Sakataren Tsaro, Pete Hegseth, ya ce manufar ba ta taba zama don canjin mulki ba kuma Mataimakin Shugaban Kasa, JD Vance, ya maimaita wannan sakon.
Maganar Trump ya haifar da ce-ce-ku-ce sosai, amma daya daga cikin tsofaffin jami’ansa ya nuna shakku kan yadda za a dauki wannan magana da muhimmanci.
Elliott Abrams, wanda ya kasance jakadan Amurka a Iran a mulkinsa na farko, ya ce akwai rudani da karkatar da magana, kuma Trump na iya kawai "yin raha" ne.
Yan majalisa sun fara maganar tsige Trump
Mun ba ku labarin cewa wasu manyan 'yan majalisa daga jam'iyyar Democrat sun caccaki Donald Trump bisa kai hari ba tare da sanar da su ba.
Hakeem Jeffries da Chuck Schumer sun bukaci amsa kai tsaye daga shugaban, suna kira da a dauki matakin hana amfani da karfin soja ba da izini ba.
Yar majalisa, Alexandria Ocasio-Cortez ta ce harin ya kai dalilan tsige shugaban kasa, tana gargadi cewa hakan zai jefa Amurka cikin yaki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng