Iran Ta Kashe Mutane a Harin Karshe zuwa Isra'ila, Ta Yaba da Jarumtar Sojojinta

Iran Ta Kashe Mutane a Harin Karshe zuwa Isra'ila, Ta Yaba da Jarumtar Sojojinta

  • Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya nuna cewa ƙasar ta amince da tsagaita wuta da shugaban Amurka Donald Trump ya sanar
  • Iran ta bayyana cewa hare-haren mayakan ta sun ci gaba har zuwa karfe 4:00 na safe, mintuna kafin fara tsagaita wutar a ranar Litinin
  • Araghchi ya gode wa dakarun Iran bisa jajircewarsu wajen kare ƙasar har zuwa lokacin na ƙarshe da aka yarda da dakatar da hare-hare

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Iran - Ƙasar Iran ta amince da shirin tsagaita wuta da shugaban Amurka Donald Trump ya sanar, a matsayin mafita ga rikicin da ya kunno kai tsakaninta da Isra’ila.

Wannan matakin ya zo ne bayan sama da mako guda na musayar hare-haren makamai tsakanin ƙasashen biyu, wanda ya janyo asarar rayuka da rushewar kadarori.

Iran ta yaba wa sojojinta bayan kammala yaki da Isra'ila.
Iran ta yaba wa sojojinta bayan kammala yaki da Isra'ila. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Legit ta tattaro bayanan da Iran ta yi ne a cikin wani sako da ministan harkokin wajenta, Abbas Araghchi ya wallafa a X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abbas Araghchi da a baya ya musanta samun wata yarjejeniya ta tsagaita wuta, ya fito yanzu yana nuna godiya ga dakarun sojin Iran bisa abin da ya kira "kare martabar ƙasa."

Trump dai ya bayyana cewa tsagaita wutar za ta fara aiki ne da misalin ƙarfe 4:00 na safe a Iran da ƙarfe 6:00 na safe a Isra’ila.

Harin da Iran ta kai na karshe zuwa Isra'ila

Kamar yadda kafar yada labarai ta BBC ta ruwaito, dakarun Iran sun kaddamar da abin da suka kira harin karshe da makamai masu linzami zuwa Isra’ila kafin fara tsagaita wutar.

An bayyana cewa harin ya auku ne kafin ƙarfe 4:00 na safe, lokacin da aka tsara fara aiwatar da yarjejeniyar dakatar da rikicin.

An rahoto cewa wasu mutane hudu sun mutu sakamakon hare-haren da aka kai a baya-bayan nan.

Araghchi ya ce:

"Ayyukan sojinmu masu ƙarfi domin hukunta Isra’ila bisa harin da ta kai sun ci gaba har zuwa minti na ƙarshe, wato ƙarfe 4:00 na safe."
Iran ta kai hari na karshe Isra'ila bayan tsagaita wuta
Iran ta kai hari na karshe Isra'ila bayan tsagaita wuta. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Iran ta gode wa sojojinta bisa jarumta

Ministan harkokin wajen Iran ya yabawa jaruman sojojin ƙasar bisa rawar da suka taka, inda ya ce sun kasance cikin shiri har zuwa ƙarshen hare-haren.

Abbas Araghchi ya ce:

"Ni da daukacin al’ummar Iran muna mika godiyarmu ga jaruman dakarunmu da suka tsaya tsayin daka wajen kare ƙasarmu har zuwa ƙarshen yakin,"

Ya kara da cewa:

“Sojojin Iran sun yi abin alfahari kuma sun nuna kwarewa da kishin ƙasa a wannan lokaci mai sarkakiya.”

Ana fatan tsagaita wutar za ta kawo karshen zubar da jini a kasashen biyu da kawo zaman lafiya mai dorewa.

Gargadin da aka yi wa Trump kan Iran

A wani rahoton, Legit Hausa ta tattaro muku jerin wasu kasashen duniya da suka yi Allah wadai da Amurka ta kai Iran.

Kasashen sun yi magana ne bayan shugaba Donald Trump ya sanar da kai hari kan cibiyoyin nukiliya a kasar Iran.

Kasar Pakistan na cikin kasashen Musulmi da suka yi Allah wadai da harin da Amurka ta kai Iran yayin da ake yaki da Isra'ila.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng