Yan Majalisar Amurka Sun Taso Trump a Gaba kan Hari a Iran, Ana Maganar Tsige Shi

Yan Majalisar Amurka Sun Taso Trump a Gaba kan Hari a Iran, Ana Maganar Tsige Shi

  • Manyan 'yan majalisa daga jam'iyyar Democrat sun caccaki Donald Trump bisa kai hari ba tare da sanar da su ba
  • Hakeem Jeffries da Chuck Schumer sun bukaci amsa kai tsaye daga shugaban, suna kira da a dauki matakin hana amfani da karfin soja ba da izini ba
  • Alexandria Ocasio-Cortez ta ce harin ya kai dalilan tsige shugaban kasa, tana gargadi cewa hakan zai jefa Amurka cikin yaki na dogon lokaci

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Washington DC, Amurka - Harin da Amurka ta kai kan Iran ya bar baya da kura musamman a majalisar tarayyar kasar.

Yan majalisar daga jam'iyyar Democrat sun caccaki Shugaba Donald Trump kan harin ba tare da sanar da su ba.

An fara maganar tsige Trump a majalisar Amurka
Yan majalisar Amurka soki harin da Trump ya kai a Iran. Hoto: Donald J Trump.
Asali: Getty Images

Yan majalisa sun taso Trump a gaba

Jaridar New York Times ta ce sun tabbatar da cewa an sanar da su ne cikin hanzari kafin hare-haren su faru inda suka soki matakin da murya daya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sun soki Trump kan yaudarar kasar musamman game da rikicin da ke faruwa tsakanin Iran da Isra'ila.

“Shugaba Trump ya yaudari kasar nan kan niyyarsa, ya kasa neman izinin Majalisa kafin amfani da karfin soja kuma ya jefa Amurka cikin hadarin shiga yaki mai illa a Gabas ta Tsakiya.

- Cewar Hakeem Jeffries

Jeffries wanda dan jam'iyyar Democrat ne daga New York kuma shugaban marasa rinjaye ya ce Trump ya kauce tsarin da ake bi.

Ya ce shugaban kasa yana da cikakken alhaki kan duk wata illa da ka iya biyo bayan wannan matakin da ya dauka shi kadai.

An soki Donald Trump kan harin Iran

Sanata Chuck Schumer, dan Democrat daga New York kuma shugaban marasa rinjaye, ya bukaci “amsoshi bayyanannu” daga Mista Trump game da harin.

Ya kuma yi kira da a kada kuri’a nan da nan kan kudurin da ke bukatar a samu cikakken izini daga Majalisa kafin amfani da karfin soja.

Wakili Jim Himes, wanda shi ne dan Democrat mafi girma a kwamitin leken asiri, ya soki harin da cewa ba bisa doka ba ne.

Ya ce:

“Shugaba Donald Trump ya yanke shawarar kai hari kai tsaye kan Iran ba tare da amincewar Majalisa ba, wanda hakan na saba wa kundin tsarin mulkin kasa.
“A wannan mataki ba za mu iya sanin ko an cimma manufofin wannan hari ba, ba ma sanin ko hakan zai janyo karin rikici a yankin da kuma hare-hare kan sojojinmu, abubuwan da za su iya jefa mu cikin yaki a Gabas ta Tsakiya.”
Ana barazanar tsige Trump bayan harin Iran
Yan majalisa suna barazanar tsige Trump kan hari a kan Iran. Hoto: Getty Images.
Asali: Getty Images

Harin Iran: An fara maganar tsige Donald Trump

Manyan 'yan Democrat da ke kula da harkokin tsaro a Majalisar ba su samu labarin hare-haren ba sai bayan Mista Trump ya wallafa su a shafinsa na sada zumunta.

Daya daga cikin fitattun ‘yan Democrat, Wakiliya Alexandria Ocasio-Cortez, ta bayyana harin a matsayin dalili na tsige shugaban kasa.

Ta ce:

“Ya yanke shawara cikin hanzari da ka iya jefa mu cikin yaki da zai dauki shekaru. Wannan tabbas dalili ne na tsige shi.

Iran ta harba rokoki bayan harin Amurka

Kun ji cewa rikicin Isra'ila da Iran ya ƙara tsananta bayan ƙasar Amurka ta kai harin bama-bamai kan cibiyoyin nukiliya uku a Iran.

Rahotanni sun nuna cewa Iran ta mayar da martani ta hanyar harba rokoki da bama-bamai kan wurare da dama a ƙasar Isra'ila.

Jami'an ceto sun tabbatar da faruwar lamarin, inda suka ce hare-haren Iran sun jikkata akalla mutane 11 kawo yanzu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.