Yan Majalisar Amurka Sun Ja Kunnen Trump bayan Ikirarin Shirin Sulhunta Iran, Isra'ila

Yan Majalisar Amurka Sun Ja Kunnen Trump bayan Ikirarin Shirin Sulhunta Iran, Isra'ila

  • 'Yan majalisar wakilai uku daga jam’iyyar Democrat sun gabatar da kuduri domin hana Donald Trump amfani da sojoji babu izini
  • Wannan ya biyo bayan harin da Trump ya kai kan cibiyoyin nukiliyar Iran, inda Iran ta mayar da martani da hari kan sansanin Amurka a Qatar
  • 'Yan majalisar sun ce ba za a bar shugaba Trump ya tayar da yaki da Iran ko wata kasa ba ba tare da izini ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Washington, DC, Amurka - Shugaban Amurka, Donald Trump ya yi jawabi ga kasa daga Fadar White House, bayan harin da sojojin Amurka suka kai kan cibiyoyin nukiliyar Iran.

Shugaba Donald Trump ya tsaya tare da sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio a yayin da yake jawabi a Washington, ranar 21 ga Yuni, 2025.

An sake taso Trump a hari kan hari a Isra'ila
Yan Majalisar Amurka gargadi Trump kan yaki da Iran. Hoto: Donald J Trump, Benjamin Netanyahu.
Asali: Getty Images

Iran/Isra'ila: 'Yan majalisa sun taso Trump a gaba

Rahoton Reuters ya ce 'yan majalisar wakilai uku na Democrat sun gabatar da kudurin hana Trump amfani da karfin soja ba tare da amincewar majalisa ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jam’iyyar Republican ta Trump na da rinjaye a Majalisar Wakilai da Majalisar Dattawa, don haka ake ganin kudurin ba zai wuce ba.

A wata sanarwa da aka fitar ranar Litinin, 'yan majalisar Jim Himes, Gregory Meeks da Adam Smith sun fadi ra’ayoyinsu.

Jim kaɗan kafin hakan, Trump ya wallafa a shafin sada zumunta cewa Isra’ila da Iran sun amince da dakatar da yaki.

“Ba za a bar Trump ya tayar da yaki da Iran ko wata kasa ba ba tare da amincewar majalisa ba."

- Cewar 'yan majalisar

An gargadi Trump kan shiga yaki da Iran
Yan Majalisa a Amurka sun gabatar da kudiri kan amfani da karfin soja. Hoto: Getty Images.
Asali: UGC

'Yan majalisar Amurka sun gano shirin Trump

Sun ce Trump ya ba da umarnin harin ba tare da tuntuba ko samun izinin majalisa ba, abinda suka kira rashin bin doka.

Wasu 'yan Democrat da Republican sun ce lokaci ya yi da za a takaita ikon Trump wajen amfani da karfin soja a Iran, cewar CBS News.

Da dama daga 'yan Democrat sun ce harin ya sabawa kundin tsarin mulki, domin ikon ayyana yaki na hannun majalisa ne.

Shugaban Majalisar Wakilai, Mike Johnson ya ce ba lokaci ba ne da ya dace a duba kudurin hana ikon yaki yanzu.

Magoya bayan Trump sun dage cewa yana da ikon kai harin domin kawar da barazanar nukiliya daga kasar Iran.

'Yan Democrat sun ce Trump ya nuna manufarsa ba domin nukiliya ba ne, tunda ya ambaci batun kifar da gwamnati.

Sun ce:

“Babu wani shiri ko tantancewa da aka yi, irin wannan lamari na bukatar tattaunawa mai zurfi, ba hanzari ba.”

'Yan majalisa sun soki Trump kan harin Iran

Kun ji cewa wasu 'yan majalisa daga jam'iyyar Democrat sun soki Shugaba Donald Trump bisa kai hari ba tare da izininsu ba.

Yan majalisar kamar su Hakeem Jeffries da Chuck Schumer sun bukaci amsa kai tsaye daga shugaban.

Sun yi kira da a dauki matakin hana amfani da karfin soja ba da izini ba wanda suka ce hakan ka iya tilasta tsige shi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.