Bayan Harin Amurka, Iran Ta Shirya Toshe Babbar Hanyar Kai Mai Kasashen Duniya

Bayan Harin Amurka, Iran Ta Shirya Toshe Babbar Hanyar Kai Mai Kasashen Duniya

  • Bayan harin Amurka, majalisar Iran ta amince a rufe mashigar ruwan Hormuz, babbar hanyar da ake kai mai kasashen duniya
  • Rufe Hormuz na iya hana jigilar ganga biliyan daya na mai a kowace rana, wanda zai sa farashin mai ya yi tashin gwauron zabi
  • Nahirar Asiya ce ake zargin za ta fi shan wahala idan aka rufe Hormuz, musamman China, Japan, Indiya, masu dogaro da man yankin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Iran - Majalisar dokokin Iran ta kada kuri'ar rufe mashigar ruwan Hormuz, wadda ta kasance babbar hanyar kai mai a kasashen duniya.

A ranar Lahadi, wani babban dan majalisar Iran ya ce, majalisar ta amince a rufe Hormuz a matsayin martani ga harin Amurka ta kai kan cibiyoyin nukiliyar kasar.

Majalisar Iran ta kada kuri'ar amince wa da rufe babbar hanyar ruwa ta Hormuz bayan harin Iran.
Ana jiran jagoran koli na Iran, Ali Hosseini Khamenei ya ba da umarnin rufe Hormuz. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Majalisar Iran ta amince a rufe Hormuz

Ɗan majalisar ya ce 'yan majalisa sun cimma matsaya kan rufe hanyar, kuma yanzu ana jiran majalisar ƙoli ta tsaron Iran ta yanke shawarar ƙarshe, inji rahoton The Guardian.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mashigar ruwan Hormuz, wadda ke bakin Tekun Fasha, tana ɗaya daga cikin muhimman hanyoyin da ake samun yawan hada-hadar jiragen mai a kasuwancin duniya.

Kimanin kashi 20 cikin ɗari na man fetur na duniya, wanda aka kiyasta kusan ganga miliyan 17 zuwa 18 a kowace rana, yana wucewa ta hanyar Hormuz.

Tasirin rufe Hormuz kan farashin man duniya

Wannan mataki na iya hana jigilar ganga biliyan daya na man fetur a kowace rana kuma ana sa ran zai sa farashin mai ya yi tashin gwauron zabi.

Ana sa ran majalisar ƙolin Iran za ta yanke shawara tare da ba da umarnin rufe mashigar da wuri, a cewar rahoton Channels.

Hormuz da ke haɗa Tekun Oman da Tekun Fasha tana da faɗin mil 20 wanda ya sa yake da sauƙin kai hari da barazanar rufewa daga Iran.

Duk da haka, rahotannin kafofin watsa labarai sun ce Iran ba ta da wani hurumi na doka don toshe zirga-zirgar ruwa ta Hormuz.

Kuma ana ganin cewa duk wani ƙoƙarin da sojojin ruwan Iran za su yi na hana amfani da mashigar Hormuz zai iya gamuwa da martani mai ƙarfi daga kasashen duniya.

Rufe Hormuz na iya hana jigilar ganga biliyan 1 na mai a kowace rana zuwa kasashen duniya
Kimanin ganga miliyan 17 zuwa 18 na kayayyakin man fetur ake wucewa da shi ta mashigar Hormuz. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Tasirin rufe Hormuz kan nahiyar Asiya

Bayan Iran, wannan hanyar ce da ake safarar mafi yawan man fetur na manyan ƙasashen yankin kamar Iraƙi, Kuwait, Qatar, Saudi Arabia da Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE).

The Economic Times ta rahoto cewa, nahiyar Asiya ce za ta fi shan wahala idan aka rufe hanyar ruwa, kasancewar China, Japan, Indiya, da Koriya ta Kudu suna samun mafi yawan man fetur da suke shigo da shi daga mashigar Hormuz.

China, wacce kawar Iran ce ta dabarun yaƙi, ita ce mai sayen man fetur mafi girma a duniya daga Iran kuma rufe wannan hanyar zai shafe ta sosai.

Tattalin arzikin Iran ma ba zai tsira daga tasirin rufe mashigar Hormz ba, amma ana ganin ta yiwu ta riga ta adana mai mai yawa da za ta yi amfani da shi a tsawon lokacin rufewar.

Amurka ta farmaki cibiyoyin nukiliyar Iran

Tun da fari, mun ruwaito cewa, Amurka ta sanar da nasarar kai hari kan cibiyoyin nukiliya guda uku a Iran, ciki har da Fordo, da nufin lalata shirin nukiliyar ƙasar.

Wannan shi ne karon farko da Amurka ta kai hari kai tsaye kan Iran, kuma hare-haren sun haɗa da jefa bama-bamai masu yawa a babbar cibiyar Fordo.

An yi amfani da jiragen B-2 stealth bombers masu ɗaukar bama-baman GBU-57, waɗanda aka san su da ƙarfin kutsawa cikin cibiyoyin da aka binne sosai a Iran.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.