Iran Ta Maida Martani bayan Harin Amurka, Ta Jefa Makamai Masu Hatsari kan Wurare 10 a Isra'ila
- Rikicin Isra'ila da Iran ya ƙara tsananta bayan ƙasar Amurka ta kai harin bama-bamai kan cibiyoyi nukiliya uku a Iran
- Rahotanni sun nuna cewa Iran ta mayar da martani ta hanyar harba rokoki da bama-bamai kan wurare da dama a ƙasar Isra'ila
- Jami'an ceto sun tabbatar da faruwar lamarin, inda suka ce hare-haren Iran sun jikkata akalla mutane 11 kawo yanzu
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Tel Aviv, Israel - Rahotanni sun tabbatar da cewa Iran ta sake harba makamai masu linzami kan ƙasar Isra'ila da safiyar ranar Lahadi, 22 ga watan Yuni, 2025
Wannan martani na zuwa ne sa'o'i ƙalilan bayan ƙasar Amurka ta jefa bama-bamai kan wuraren makamashin nukiliyar Iran guda uku.

Asali: Getty Images
Makamai masu linzami sun tunkari Isra'ila
Al-Jazeera ta rahoto cewa rundunar sojin Isra'ila ta ankarar da mazauna ƙasar cewa ta hango makamai masu linzami sun tunkaro daga Iran.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dakarun soji na Isra’ila sun bayyana cewa sun gano wani sabon jerin makamai masu linzami daga Iran da ke tunkarar ƙasar, don haka mutane su nemi mafaka.
Hukumomin Isra’ila sun sake jan hankalin jama’a da su “guji wallafawa ko yada wurare da bidiyo” na harin da aka kai masu.
Jim kaɗan bayan haka kuma, sashen kare lafiyar fararen hula na Sojojin Isra’ila ya sanar cewa yanzu mutane za su iya fitowa daga wuraren buya, alamar cewa harin makamai daga Iran ya ƙare.
An bayyana cewa ma’aikatan ceto suna aiki a sassa daban-daban na ƙasar “inda aka samu rahoton faɗawar makamai.”
Iran ta jefa bama-bamai kan wurare 10
A nasu ɓangare, jami'an ba da agajin gaggawa sun bayyana cewa Iran ta yi nasarar jefa bama-bamai a wurare 10 a ƙasar Isra'ila da safiyar nan.
Wani mai magana da yawun ma’aikatan ceto na Isra’ila ya ce rahotannin farko sun nuna cewa rokoki da ƙwayoyin fashewa sun faɗa a wurare 10 a ƙasar.
Wannan ya haɗa da yankunan Carmel, Haifa, yankin Tel Aviv, da tekun Arewacin ƙasar Isra'ila.
Yahudawa 16 sun jikkata a Isra'ila
Mutane 11 ne aka tabbatar da sun jikkata a Isra’ila sakamakon harin makamai daga Iran, kuma yanzu haka suna karɓar kulawar likitoci.
Rahoton The Times of Israel ya ambato cibiyar agajin gaggawa ta ƙasa MDA na cewa:
"Ɗaya daga cikin mutanen da aka jikkata ya sami raunuka ne sakamakon fashewar bam, sauran mutum 15 kuma raunin da suka samu masu sauƙi ne."
Amurka ta kai hari farko kan Iran
A wani labarin, kun ji cewa a karon farko tun bayan ɓarkewar rikici, Amurka ta kai hare-hare kan cibiyoyin nukiliya a Iran.
Shugabana Amurka, Donal Trump ne ya tabbatar da haka ranar Asabar, yana mai cewa lokacin ya yi da Iran za ta ajiye makamai ta rungumi sulhu.
Ana ganin wannan hare-hare da Amurka ta kai na iya ƙara rura wutar rikici tsakanin Iran da Isra'ila wanda ya fara a ranar Juma'a, 13 ga Yuni, 2025.
Asali: Legit.ng