A harbe duk wani jirgin ruwan Iran da ya yi mana barazana – Inji Donald Trump

A harbe duk wani jirgin ruwan Iran da ya yi mana barazana – Inji Donald Trump

A tsakiyar makon nan ne shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya sake fitowa shafinsa na sada zumunta na Tuwita ya sanar da Duniya wani mataki mai razanarwa da ya dauka.

Donald Trump ya bada umarni ga sojojin ruwan Amurka su budawa jiragen kasar Iran da ke cikin ruwa wuta. Wannan na zuwa ne bayan takaddamar da ake samu a yankin Gabas.

“Na bada umarni ga sojojin ruwan Amurka su harbe, su yi raga-raga da duk wani jirgin ruwan kasar Iran idan ya yi wa jiragen mu barazana a cikin ruwa.” Inji Shugaban Amurka.

Kafin yanzu Amurka ta ce wasu jiragen sojojin juyin juya-halin Iran su na tunkararsu. Sojojin Amurkan sun zargi wadannan jirage na dakarun kasar Iran da yi mata barazana.

Rundunar sojin ruwan Amurka ta ce wani lokaci jiragen Iran su kan tunkari jiragen Amurka da ke cikin ruwa a guje har ta kai saura kusan mita tara ne tazarar da ke tsakaninsu.

KU KARANTA: Gwamnatin Amurka ta kai Sin kotu a kan barkewar annobar COVID-19

A cewar jami’an sojin ruwan na Amurka da kyar su ka yi kokari su ka kaucewa jiragen Iran. Sojojin sun ce ba dan dabarun da su ka yi ba, da wasu sun mutu a sanadiyyar hakan.

Dangatakar da ke tsakanin kasashen ta na kara yin haba-haba. Gwamnatin kasar Amurka da Donald Trump sun dauki sojojin juyin-juya-halin Iran ne a matsayin ‘yan ta’adda.

Wannan barazana da ta fito daga bakin shugaban Amurka Trump ta zo ne jim kadan bayan wadannan sojin kasar Iran sun harba wani tauraron ‘dan-adam zuwa sararin samaniya.

A ranar Laraba, 22 ga watan Afrilu, 2020, Iran ta maidawa Donald Trump martani. Kasar Iran ta fadawa Amurka ta janye dakarun sojojin da ta baza a cikin kasashen gabas ta tsakiya.

Mai magana da bakin sojojin Iran, Abolfazl Shekarchi ya yi kira ga gwamnatin Donald Trump ta ceto rayukan mutanen da cutar COVID-19 ta ke kashewa, ta daina zarewa kasashe ido.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel