Hafsan Tsaro Ya Gano yadda Makwabta ke Ta'azzara Ta'addanci, Ya Bukaci a Katange Najeriya
- Babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya ce iyakar Najeriya da Jamhuriyar Nijar ce mafi rauni da hadari
- Ya bayyana a kan yadda 'yan ta'adda ke amfani da wannan dama wajen kwararowa cikin kasar, tare da hana mutane sakat
- Janar Christopher Musa ya bukaci a gina katanga tare da amfani da fasahar zamani kamar kyamarori don magance matsalar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya bayyana cewa iyakar Najeriya da Jamhuriyar Nijar na da hadari da rauni.
Ya ce wannan ya sa 'yan ta'adda ke samun damar tsallakowa zuwa cikin Najeriya, wanda ke bukatar a dauki matakin gaggawa domin dakile lamarin.

Asali: Facebook
Janar Musa ya bayyana haka ne a wata hira da aka yi da shi a tashar Arise News a ranar Alhamis, yayin da yake tattauna ƙalubalen tsaro da ƙasar ke fuskanta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce daya daga cikin hanyoyin da za a bi wajen dakile matsalar shi ne, a gina katanga a tsakanin Najeriya da Nijar, da sauran iyakokin kasar nan.
'Yan ta'adda na kwararowa Najeriya,' Hafsan Tsaro
Jaridar Punch, Janar Chirstopher Musa ya bayyana cewa kungiyoyin ta’addanci kamar Boko Haram da ISWAP na amfani da raunin iyakokin kasar nan wajen kara shigo wa.
Ya ce:
“Bayan nazari da na yi kan yankin Sahel, na gano cewa babban burin ’yan ta’adda da ’yan bindiga shi ne Najeriya."
“Akwai hare-hare daga Burkina Faso, sannan a Jamhuriyar Benin akwai tazarar kilomita 50 kacal zuwa Najeriya, nan ma wuri ne mai hadari sosai.”
Janar Christopher: Najeriya na wahala da yan ta'adda
Janar Musa ya kuma jaddada cewa matsayin Najeriya a matsayin ƙasa mai magana da Turanci wacce ke kewaye da ƙasashen da ke magana da Faransanci na ƙara tsananta barazanar tsaro.

Asali: Facebook
Ya ce:
“Muna kewaye da ƙasashe masu magana da Faransanci. Manufofi da dabarunmu sun bambanta. Don samun tsaro, dole ne mu gina katanga a kan iyakokinmu."
Yayin da wasu ke nuna damuwa kan yawan kuɗin da za a kashe wajen gina irin wannan katanga, Janar Musa ya ce tsaro ya fi komai muhimmanci.
“Wasu na cewa kuɗi da yawa za a kashe. Amma me kuɗi ya zama idan kana cikin hatsari ko ka mutu? Ƙasashen da suka yi nazari sun fahimci cewa dole ne su kare kansu."
"Idan ka gina katanga kuma ka haɗa da fasahar zamani, kamar su kyamarori da jiragen leƙen asiri, za a rage buƙatar ma’aikata a wancan yankin.”
Sojojin Najeriya sun fatattaki 'yan ta'adda
A baya, mun wallafa cewa dakarun rundunar sojojin ruwa na Operation Hadin Kai (OPHK) sun dakile wani mummunan hari da wasu da ake zargin 'yan Boko Haram suka kai a sansaninsu.
Maharan sun kai farmaki ne da misalin 2.00 na dare da nufin mamaye sansanin da lalata injinan ruwa da gwamnatin Jihar Borno ta girka domin gyara hanyoyin ruwa a yankin tafkin Chadi.
Sai dai sojoji sun yi ƙwazo, inda suka shafe tsawon sa’o’i biyu ana gwabzawa, sannan aka samu nasarar kora 'yan ta'addan bayan an yi masu illa da dakile aniyarsu ta mamaye sansanin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng