Yadda Donald Trump Ya Daƙile Shirin Isra'ila na Hallaka Jagoran Iran, Khamenei

Yadda Donald Trump Ya Daƙile Shirin Isra'ila na Hallaka Jagoran Iran, Khamenei

  • Wani babban jami'in gwamnatin Amurka ya fadi abin da Donald Trump kan shirin Isra'ila kan kasar Iran
  • Jami'in ya ce Trump ya hana Isra’ila kashe jagoran addini a Iran, Ayatollah Ali Khamenei, duk da shirin da suka tsara
  • Trump ya ce Amurka ba ta da hannu a hare-haren, amma zai iya shiga yakin idan Iran ta kai hari, yana mai rokon a nemi sulhu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Washington DC, Amurka - Shugaban Amurka Donald Trump ya hana wani shirin kasar Isra’ila na kashe jagora a kasar Iran.

Wani babban jami'in gwamnatin Amurka ya ce Trump ya ki amincewa da shirin kisan Ayatollah Ali Khamenei.

Trump ya dakile shirin Isra'ila kan Iran
Abin da Trump ya yi da ya gano Isra'ila na shirin hallaka jagora a Iran. Hoto: Getty Images.
Asali: Getty Images

Yadda Trump ya hana kisan Khamenei

Hakan na cikin wani rahoto da jaridar Reuters ta kawo inda ta ce Trump ya tsame hannunsa kan shirin da Iran ta yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Isra’ila ta shaida wa gwamnatin Trump a kwanakin baya cewa sun kammala tsara wani sahihin shiri na kashe Khamenei.

Bayan an gabatar da cikakken bayani kan shirin, Fadar White House ta bayyanawa jami’an Isra’ila cewa Trump ya ki amincewa da daukar wannan mataki.

A cewar wani jami’i da ba a ba shi izinin yin sharhi kan lamarin ba, kuma ya yi magana ne a kan sharadin a boye sunansa.

Jami'in gwamnatin ya ce:

“Muka gano Isra’ila na da shirin kashe jagoran Iran.
"Shugaba Trump ya ki amincewa, mun fada musu ka da su ci gaba da aiwatar da shirin."

Da safiyar Lahadi, Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya guje wa amsa tambaya kan cewa Trump ya hana kashe Khamenei.

Ya ce:

“Ba zan ce komai a kai ba, amma zan ce mu na yin abin da ya dace kuma Amurka na fahimta.”
Rawar da Trump ya taka game da shirin Isra'ila kan Iran
Donald Trump ya hana shirin Isra'ila na kashe Ali Khamenei. Hoto: Getty Images.
Asali: Getty Images

Musayar wuta tsakanin Isra'ila da Iran

Wannan na zuwa ne yayin da Isra’ila da Iran ke ta musayar hare-hare da makamai, inda an umurci jama’a su shiga mafaka, har a birnin Tehran.

Yakin da aka dade ana yi ta hanyar wakilai da leƙen asiri ya rikide zuwa yaki na gaba da gaba da ke tayar da hankalin duniya, cewar The Washington Times.

Yakin ya fara ne ranar Juma’a lokacin da Isra’ila ta kai hari wanda ya kashe manyan hafsoshi da masana nukiliya da kuma fararen hula.

Firaminista Netanyahu ya ce za su saka Iran daukar alhakin abin da suka aikata saboda kashe fararen hular Isra’ila a harin da suka kai.

Ya kuma ce sun kashe shugaban leken asirin Iran, Mohammad Kazemi da mataimakinsa yayin da jiragen su ke kai hare-hare a Tehran.

Iran ta toshe hanyar jigilar mai kasashe

Kun ji cewa dakarun Iran sun ayyana rufe mashigin ruwa na Hormuz, suna cewa babu wani jirgin ruwa da zai bi ta yankin har sai da izini daga gwamnati.

Wannan mataki na zuwa ne bayan harin da Isra’ila ta kai kan Iran da nufin hana ta mallakar makamin nukiliya.

Kasashen Turai da hukumomin sufurin jiragen ruwa sun fara gargadin jiragen su da su guji yankin saboda yiyuwar barkewar rikici mafi muni.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.