Matashi Ya Yi wa Mahaifiyarsa Jina Jina da Sanda har Ta Mutu a Benue
- Wani matashi mai suna Torngusha Usuwe ya shiga hannu bayan zargin dukan mahaifiyarsa da sanda har ta mutu a Gungul, karamar hukumar Ukum ta jihar Benue
- Rahotanni sun ce rigima ta ɓarke tsakaninsu a cikin gida, wanda ya sa ya buge mahaifiyarsa a habar hagu da sanda daga nan kuma aka kai ta asibiti
- Bayan mutuwar matar, jami’an ‘yan sanda sun kai samame, suka kama wanda ake zargi kuma yanzu haka an adana gawar domin gudanar da bincike
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Benue - Rundunar ‘yan sanda a jihar Benue ta tabbatar da cafke wani matashi, Torngusha Usuwe, bisa zargin kashe mahaifiyarsa a cikin garin Gungul da ke karamar hukumar Ukum.
Rahotanni sun nuna cewa rikici ya ɓarke tsakanin Torngusha da mahaifiyarsa a ranar Talata da misalin karfe 2:30 na rana, wanda ya haifar da dukan da ya kai ga mutuwar matar.

Asali: Original
Legit ta tattaro bayanai kan lamarin ne a cikin wani sako da mai sharhi kan tsaro, Zagazola Makama ya wallafa a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Binciken farko ya nuna cewa matashin ya buge mahaifiyarsa a habar hagu da sanda, wanda hakan ya haddasa mummunan rauni da jini ya fara zuba daga bakin da kunnen matar.
An garzaya da ita asibiti amma rai ya yi halinsa
Bayan aukuwar lamarin, makwabta da dangin marigayiyar sun garzaya da ita zuwa cibiyar lafiya ta Zege Nyion da ke Gungul domin samun taimakon gaggawa.
Sai dai likitoci sun tabbatar da rasuwarta da misalin karfe 8:00 na dare a ranar da lamarin ya faru, duk da kokarin da aka yi na ceto rayuwarta.
Wani dan uwan marigayiyar, Terwase Usuwe, ne ya kai rahoton lamarin ga hukumomin tsaro, wanda hakan ya sa aka tura jami’an bincike zuwa wajen da abin ya faru.
An kama wanda ya kashe mahaifiyarsa a Benue
Rundunar ‘yan sanda ta ce an dauki hotunan wajen da abin ya faru tare da dauke gawar zuwa dakin ajiye gawarwaki na Gungul domin gudanar da binciken asibiti.
Kakakin rundunar ya tabbatar da cewa wanda ake zargin, Torngusha Usuwe, yana hannun hukuma domin ci gaba da bincike.
Hukumomin tsaro sun ce ana gudanar da bincike mai zurfi domin gano ainihin dalilan da suka kai ga wannan kisan gilla da kuma tantance ko akwai wasu da suka hada kai da shi.

Asali: Facebook
Lamarin ya tayar da hankali a yankin Gungul, inda mazauna suka bayyana damuwarsu kan yadda rikice-rikicen cikin gida ke rikidewa zuwa manyan laifuffuka.
Matashi ya kashe mahaifinsa a Jigawa
A wani rahoton, kun ji cewa wani matashi ya kashe mahaifinsa a unguwar bakin kasuwa da ke yankin Sara a Gwaram ta jihar Jigawa.
Rahoton da ya sanda suka fitar ya nuna cewa matashin ya yi amfani da wuka ne ya sara mahaifin na shi.
Rahotanni sun tabbatar da cewa 'yan sanda sun samu nasarar cafke matashin tare da cigaba da masa tambayoyi kan zargin da ake masa.
Asali: Legit.ng