Tinubu da Musulman Shugabanni da Suka Halarci Rantsar da Fafaroma Leo XIV
Manyan shugabannin duniya, ciki har da Musulmai sun halarci taron bikin rantsar da sabon Fafarom da aka gudanar a Vatican.
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - An yi bikin rantsar da Fafaroma Leo XIV a fadar Vatican a ranar Lahadi, 18 ga watan Mayu, 2025.
Manyan shugabanni daga kasashen duniya daban daban sun halarci bikin shan rantuwar da sabon Fafaroman ya yi.

Asali: Getty Images
A wannan rahoton, Legit ta tattaro muku jerin shugabannin Musulmi da suka halarci taron ko suka tura wakilai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. Bola Tinubu ya je bikin nada Fafaroma
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya halarci bikin rantsar da sabon shugaban cocin Katolika na duniya, Fafaroma Leo XIV, a dandalin St. Peter da ke birnin Vatican a Rome a kasar Italiya.
Bikin ya kasance na musamman domin yana nuna fara jagorancin sabon Fafaroma bayan rasuwar Fafaroma Francis.
Tinubu ya samu gayyata ne daga Fafaroma Leo XIV, wanda ya bayyana Najeriya a matsayin kasa da ta kasance kusa da zuciyarsa tun lokacin da ya taba aiki a Ofishin Jakadancin Vatican a Lagos.
Vanguard ta wallafa cewa shugaba Tinubu ya bayyana cewa halartar bikin yana daga cikin kokarinsa na karfafa hadin kai da fahimtar juna a Najeriya, yana mai cewa:
"Yana daga cikin hanyar hadin kai duk da bambance bambancenmu."

Asali: Twitter
Tinubu ya gana da wasu manyan ‘yan adawa a Najeriya, ciki har da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP, Peter Obi, da tsohon gwamnan jihar Ekiti, Dr Kayode Fayemi.
Mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai, ya wallafa a X cewa Fayemi ne ya hango Tinubu a wurin, sannan ya gayyaci Obi su je su gaishe da shugaban kasar.
Fayemi ya yi raha da cewa:
“Ya shugaban kasa, barka da zuwa cocinmu,”
Sai Tinubu ya amsa cikin dariya da cewa:
“Ya kamata ni zan tarbe ku, ni ne shugaban tawagar Najeriya baki daya.”
Bayan rantsar da Fafaroman, Shugaba Bola Tinubu ya gana da wakilan malaman cocin Katolika na Najeriya (CBCN) a Rome.
Tinubu ya jaddada cewa bai kamata bambancin addini da kabila ya raba al’umma ba, ya fi kamata ya zama hanyar ci gaba da hadin kai.
Sai dai wasu masu amfani da kafafen sadarwa sun nuna rashin jin dadin ganin shugaban kasar a Vatican, musamman ganin ya yi amfani da tikitin Muslim Muslim.
2. Shugaban Albania ya je nadin Fafaroma
Shugaban kasar Albania, Bajram Begaj, ya jagoranci tawagar kasarsa zuwa bikin rantsar da Fafaroma Leo XIV.
A yayin da ya halarci bikin tare da wasu manyan jami’an gwamnatin kasar Albania, Shugaba Begaj ya gana da Fafaroman.
Bajram Begaj ya taya Fafaroma Leo murna bisa zabensa a matsayin sabon shugaban cocin Katolika na duniya.

Asali: Twitter
Rahoton Euro News Albania ya nuna cewa shugaba Begaj ya kasance tare da Ministan Harkokin Wajen kasar, Igli Hasani, da jakadiyar Albania Vatican, Majlinda Frangaj a wajen taron.
Wani rahoto da kasar Amurka ta wallafa ya nuna cewa kashi 70 na mutanen kasar Albania Musulmai ne kuma galibinsu Sunni.
Haka zalika daga kasar Albania fitaccen malamin Musulunci da ya shahara a duniya, Sheikh Nasirudden Albani ya fito.
3. Fira Ministan Morocco ya je nadin Fafaroma
Daga cikin manyan baki da suka halarci bikin nada Fafaroma akwai Firaministan Morocco Aziz Akhannouch, wanda ya wakilci Sarki Mohammed VI.
Rahoton North African Post ya nuna cewa bayan kammala taron, Akhannouch ya gana da sabon Fafaroma Leo XIV tare da wasu shugabanni da wakilai daga kasashen duniya.

Asali: Getty Images
Sarki Mohammed VI ya aiko da sakon taya murna ga sabon Fafaroma, yana mai cewa nadinsa ya zo a lokacin da ake bukatar hadin kai da fahimta tsakanin mabiya addinai.
Fafaroma Leo ya yi kira ga zaman lafiya
A wani rahoton, kun ji cewa sabon Fafaroma da aka nada a Vatican ya bukaci a kawo zaman lafiya a duniya.
Fafaroma Leo ya bukaci kawo karshen rikicin da aka dade ana fama da shi a Gaza da wasu sassan duniya.
Legit ta rahoto cewa sabon Fafaroman ya yi maganar ne a cikin hudubar farko da ya gabatar kafin shan rantsuwar fara aiki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng