Hajji: An Kaddamar da Manhajar Kur'ani Mafi Girma a Duniya a Saudiyya

Hajji: An Kaddamar da Manhajar Kur'ani Mafi Girma a Duniya a Saudiyya

  • Hukumomin kula da harkokin addini a Masallacin Manzon Allah (SAW) sun kaddamar da shahararriyar manhajar koyar da Alkur’ani mafi girma a duniya
  • An kaddamar da shirin ne a ribibin fara aikin Hajjin bana, kuma manhajar za ta mayar da hankali kan haddar Kur’ani, karanta shi da kuma fahimtar shi
  • Limamin Harami, Abdulrahman Al-Sudais ya ce burin shirin shi ne zurfafa soyayya da fahimtar Kur’ani a zukatan alhazai da al’ummar Musulmi gaba ɗaya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Saudi Arabia - A wani babban mataki na bai wa Alkur’ani girma da muhimmanci a lokacin aikin Hajji, Saudiya ta kaddamar da wani shiri na musamman.

Rahotanni sun nuna cewa shirin shi ne mafi girma a duniya dangane da koyar da Alkur’ani mai tsarki.

Kur'ani
An kaddamar da sabuwar manhajar Kur'ani a Saudiyya. Hoto: Getty Image
Asali: UGC

Gulf News ta rahoto cewa an sanar da kaddamar da shirin ne ta bakin shugaban harkokin addini na Masallacin Harami, Sheikh Dr Abdulrahman bin Abdulaziz Al-Sudais.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shirin zai taimaka wajen kusantar da alhazai da kuma al’ummar Musulmi gaba ɗaya kusa da Alkur’ani mai tsarki ta hanyar karatu, nazari, da kuma kyakkyawan fahimta.

Yadda aka tsara shirin Kur'ani a Saudiyya

Al-Sudais ya bayyana cewa an tsara shirin cikin manyan hanyoyi da dama, ciki har da tallafa wa da’irar haddar Qur’ani, rubuce-rubucen ilimi, da kuma amfani da manhajojin zamani.

Manhajar na dauke da dandalin zamani na koyar da Alkur’ani da aka tsara bisa turbar shari’a kuma an tabbatar da sahihancinsa.

Rahoton Daily Trust ya nuna cewa ana amfani da sababbin fasahohin kere-kere irin su AI domin inganta koyarwar manhajar.

Manhajar za ta rika ba da cikakken bayani kan karatun Qur’ani da kuma haddar shi, tare da kulawar malaman da suka kware kuma suka dace da irin aikin.

Yadda za a koyi Kur'ani ta manhajar Saudiyya

Shirin ya kuma tanadi hanya ta musamman ga wadanda ke son koyon Qur’ani daga ko’ina a duniya ta hanyar intanet, inda za a iya shiga darussa daga wurare daban-daban na duniya.

An bayyana cewa shirin zai kasance dandalin zurfafa fahimtar koyarwar Alkur’ani, musamman game da akidun addini, da halaye masu kyau, da kuma fahimtar matsakaicin tafarkin Musulunci.

Makkah
Mahajjata za su ci moriyar sabuwar manhajar Kur'ani a Saudiyya. Hoto: Inside the Haramain
Asali: Facebook

Sheikh Al-Sudais ya ce:

“Shirin zai zama jagora a duniya wajen yada karatun Qur’ani cikin sauki, da nufin tabbatar da fahimtar gaskiya da matsakaicin tafarki cikin al’umma.”

Ya kara da cewa hakan na daya daga cikin muhimman burin kasar Saudiya na samar da cibiyar addini da ilimi wacce za ta rika amfanar da Musulmi daga sassa daban-daban na duniya.

Donald Trump ya ziyarci kasar Saudiyya

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya kai wata ziyarar aiki kasar Saudiyya.

Shugaba Donald Trump ya tattauna da mahukuntan kasar Saudiyya game da lamuran tsaro, zuba jari da sauransu.

Ziyarar dai na cikin jerin ziyarce ziyarce da shugaba Donald Trump ya fita yi kasashen Larabawa da suka hada da Qatar da UAE.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng