Donald Trump Ya Dura Saudiyya yayin da Mahajjata ke Isa Kasar daga Sassan Duniya

Donald Trump Ya Dura Saudiyya yayin da Mahajjata ke Isa Kasar daga Sassan Duniya

  • Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya isa Saudiyya a wata muhimmiyar ziyara ta kwana uku da zai kai har Qatar da Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE)
  • Yarima mai jiran gado, Mohammed bin Salman (MBS), ya tarbi Trump a Riyadh, ana sa ran za su kulla yarjejeniyoyi masu muhimmanci da za a sanar daga baya
  • An ce batutuwa da za su tattauna sun haɗa da harkokin kasuwanci, zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya, da halin da ake ciki a Gaza da Syria da sauransu

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Saudi Arabia - Shugaban Amurka, Donald Trump, ya kaddamar da wata muhimmiyar ziyara ta kasa da kasa da ta fara a Saudiyya.

Da isar Trump Saudiyya, Yarima mai jiran gado, Mohammed bin Salman ya tarbe shi a birnin Riyadh.

Trump
Trump ya kai ziyara kasar Saudiyya. Hoto: AFP
Asali: AFP

Rahoton Al-Jazeera ya nuna cewa ziyarar za ta ƙunshi mahawara kan huldar tattalin arziki da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Baya ga haka, ziyarar za ta mayar da hankali kan dangantakar diflomasiyya tsakanin Amurka da ƙasashen Larabawa kamar yadda rahoton New York Times ya nuna.

An shirya ziyarar ne domin ƙarfafa zumunci tsakanin ƙasashen biyu, tare da gayyatar shugabannin ƙasashen GCC domin ci gaba da tattauna manyan batutuwa na yankin.

An tarbi Trump a fadar masarautar Saudiyya

Shugaba Trump ya isa Fadar Sarauta da ke Riyadh tare da rakiyar mahaya doki da ke ɗauke da tutar Amurka da Saudiyya.

A yayin bikin tarbar, an buga taken ƙasa na Amurka a gaban shugaban da Yarima Mohammed bin Salman a wani dakin taro.

Daga bisani, Trump da MBS sun shiga babban dakin taron inda ake sa ran za su kulla yarjejeniyoyin kasuwanci da diflomasiyya kafin sanarwa daga baya a yau.

Maganar zuba jarin Saudiyya a Amurka

Babban abin da ke saman manufar ganawar ita ce yarjejeniyar kasuwanci. MBS ya ce Saudiyya na shirin zuba jari har na $600bn a Amurka, yayin da Trump ke son samun $1trn daga Saudiyya.

A cewar rahotanni, ana kokarin kammala tattaunawa kan adadin kudin da Saudiyya za ta zuba a cikin tattalin arzikin Amurka.

Taron zuba jari tsakanin Amurka da Saudiyya zai gudana yau a Riyadh, inda manyan jami’ai da ‘yan kasuwa daga ɓangarorin biyu za su halarta.

Trump
Trump zai tattauna batun zaman lafiya a Saudiyya. Hoto: Getty images
Asali: Getty Images

Tattaunawa kan zaman lafiya da siyasa

A gefe guda, za a tattauna batutuwan siyasa, musamman matsalolin Gaza, rikicin Syria da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya.

A cewar jami’an Saudiyya, akwai buƙatar haɗin gwiwa da daidaituwar matsaya domin fuskantar ƙalubalen da ke gaban ƙasashen yankin.

Wannan ne ya sa ake gayyatar shugabannin ƙasashen GCC domin shiga cikin tattaunawar da za a ci gaba da yi a gobe Laraba.

Trump ya fusata Kiristocin duniya

A wani rahoton, kun ji cewa Kiristoci a fadin duniya sun yi Allah wadai da wani aikin shugaban Amurka, Donald Trump.

Hakan ya biyo bayan wani hoto da shugaban kasar ya wallafa a shafinsa na X sanye da kayan Fafaroma.

Kiristoci sun ce bai kamata shugaba Donald Trump ya sanya hoton ba a daidai lokacin da ake cikin jimamin rasuwar Fafaroma Francis.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng