An Samu Gwaraza a Gasar Karatun Al-Kurani da Aka Yi a Kwara

An Samu Gwaraza a Gasar Karatun Al-Kurani da Aka Yi a Kwara

  • Bayan baje kolin ilimi tare da samun nasara a zagaye daban-daban, an samu zakaru a zagayen karshe na karatun Al-Kur'ani a jihar Kwara
  • An gudanar da gasar ne a matakin rukunai na daya zuwa na biyar da suka shafi hizib 60 da tajwidi, tafsiri, kira'a da tangimi, a bangaren maza da mata
  • Kwamitin gudanar da gasar ya roki gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq, da ya bayar da filin gina cibiyar haddar Alkur’ani a jihar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Kwara - An samu gwarazan da suka yi nasara a zagayen karshe na gasar karatun Al-Kurani ta shekarar 2023 a jihar Kwara.

An gudanar da zagayen karshe na gagarumar gasar a filin wasa na garin Ilorin.

Kara karanta wannan

Ku kara hakuri, Tinubu na da shirin ciyar da kasar nan gaba, shawarin minista ga 'yan Najeriya

Kwara/Karatun Al-Kur'ani
An samu gwarazan da suka yi nasara a zagayen karshe na gasar karatun Al-Kurani ta shekarar 2023 a jihar Kwara. Hoto: @BMB_Official1
Asali: Twitter

Gasar Al-Kur'ani: Zakaru a bangaren maza

A bangaren maza, Haroon Hassan ne ya zama zakara a rukunin farko na hizib 60 da tajwidi, tafsiri da kira’a, Leadership ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A rukuni na biyu kuwa, Abdullateef Zakariyyah ya zo na daya a bangaren hizib 60 da Tajwidi da tafsiri.

A rukuni na uku na hizib 60 tare da tajwidi, Uthman Uthman ne ya samu nasara a daidai lokacin da Sherifdeen Zakariyyah ya zama zakara a rukuni na hudu na hizib 30 tare da tajwidi.

Rukuni na 5 na hizib 10 tare da tangimi da tajwidi, Hussein Ibrahim ne ya samu nasara.

Gasar Al-Kur'ani: Zakaru a bangaren mata

A bangaren mata, Aishat Adekanye ce ta zo na daya a rukuni na 3 na hizib 60 tare da tajwidi, yayin da Jemilat Tijani ta samu nasara a rukuni na hudu na hizib 30 da tajwidi.

Kara karanta wannan

Abin kunya yayin da dan takarar gwamna a jam'iyyar NNPP ya shiga hannu kan zargin damfarar N607m

A rukuni na 5 na hizib 10 tare da tangimi da tajwidi, Maryam Issa ce ta samu nasara.

A jawabinsa, shugaban kwamitin karatun Al-kur’ani na jihar, Alhaji Shehu AbdulGafar, ya yabawa Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq bisa tallafin kudi da kwarin guiwa da ya bai wa kwamitin.

Sai dai ya roki gwamnan da ya gaggauta amincewa da bayar da filin gina cibiyar haddar Alkur’ani a jihar.

Gwamnatin Birtaniya za ta ba daliban Najeriya tallafi

A wani labarin da Legit Hausa ta ruwaito, daliban Najeriya na da damar neman tallafin Euro 10,00 daga gidauniyar GREAT don yin karatun PGD a jami'o'in kasar Burtaniya a zangon karatu na 2024-25.

Wannan tallafin hadin guiwa ne tsakanin gidauniyar GREAT Britain da kuma hukumar kasar Birtaniya, da suka shafi jami'o'in Ingila, Wales, Scotland da Ireland ta Arewa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel