Saudiyya: Ɗan Sarki da Bai cikin Hayyacinsa dalilin Hatsari Ya Cika Shekaru 20 Yana Bacci

Saudiyya: Ɗan Sarki da Bai cikin Hayyacinsa dalilin Hatsari Ya Cika Shekaru 20 Yana Bacci

  • Dan Sarki, Al-Waleed bin Khaled bin Talal, wanda ake kira "Sarkin Barci," ya cika shekara 20 a duniya bai cikin hayyacinsa bayan hadarin mota a 2005
  • An ce likitoci sun ba da shawarar a cire na'urorin taimakon numfashi a 2015, amma mahaifinsa ya ki, yana fatan samun mu'ujiza
  • A 2019, Al-Waleed ya nuna dan motsi kamar daga yatsa ko juya kai, amma rahotanni sun ce ba a samu ci gaba ba bayan haka
  • A ranar zagayowar ranar haihuwarsa cika shekaru 36, mutane da dama a dandalin X sun yi addu'o'i da fatan Allah ya sa ya farfado

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Riyadh, Saudiyya - Dan Sarki, Al-Waleed bin Khaled bin Talal na Saudiyya, wanda aka fi sani da "Sarkin Barci," ya cika shekara 36 a makon da ya gabata.

Matashin ɗan biloniya Khaled bin Talal, ya suma bayan wani haɗarin mota a 2005 yayin karatu a Kwalejin Sojoji a Birtaniya inda har yanzu yake kwance.

Dan Sarki ya shekara 20 a sume a Saudiyya
Dan Sarki a Saudiyya ya shafe shekaru 20 bai cikin hayyacinsa bayan hatsarin mota. Hoto: @DevalPatel1100.
Asali: Twitter

Saudiyya: Yaushe ɗan Sarki ya yi hatsari?

Hakan na cikin wata sanarwa da shafin Your Desire ya wallafa a shafin X a yau Lahadi 27 ga watan Afrilun 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tun 2005 da ya yi hatsari aka sanya shi a kan na'urorin taimakon numfashi a Riyadh da ke kasar Saudiyya ana ciyar da shi ta bututu tsawon shekaru kusan ashirin.

A 2015, likitoci sun ba da shawarar a cire na'urorin, amma mahaifinsa ya ƙi, yana cewa, 'idan Allah na so ya mutu, da ya mutu lokacin hatsarin'.

A 2019, rahotanni sun ce ya yi dan motsi kamar daga yatsa ko juya kai, amma babu wani ci gaba tun daga lokacin.

Wani tsohon bidiyon 2019 da ke nuna shi yana motsa kansa karo na farko ya sake bayyana kuma ya bazu sosai a shafukan sada zumunta.

Al-Waleed bin Khaled bin Talal yana cikin dangin sarakunan Saudiyya, amma ba ɗa ko ɗan'uwan Sarki Salman ba ne kai tsaye.

Kakansa, Talal bin Abdulaziz Al Saud, ɗaya ne daga cikin 'ya'yan Sarkin Abdulaziz Al Saud, wanda ya kafa kasar Saudiyya.

Matashin dan Sarki a Saudiyya yana ci gaba da bacci bayan shekaru 20
Dan Sarki yana ci gaba da bacci shekaru 20 kenan bayan hatsarin mota. Hoto: Saudi Gazette.
Asali: UGC

An yiwa dan Sarki addu'o'in cika shekaru 36

A ranar zagayowar haihuwarsa shekaru 36 a bana, mutane a dandalin X sun yi addu'o'i suna rokon Allah ya sa 'Sarkin Bacci' ya farfado lafiya.

Wani mai amfani da X ya ce:

"Ina fata zai farka nan kusa. Allah madaukaki ya albarkace shi."

Wani kuma ya rubuta:

"Lallai zai dawo hayyacinsa. Allah ya cika burin mahaifiyarsa, Ameen."

Mahajjata 43,000 za su fara tashi zuwa Saudiyya

Kun ji cewa hukumar NAHCON da shugabannin hukumar jin daɗin alhazai na jihohi sun cimma matsaya kan fara jigilar mahajjata ranar 9 ga Mayun 2025.

Hukumar ta ware alhazai 43,000 zuwa kamfanonin jiragen sama huɗu da za su yi jigilar hajjin bana zuwa kasar Saudiyya mai tsarki.

NAHCON ta ja kunnen jihohi da su guji rajistar mata masu juna biyu, tana mai cewa an tanadi cibiyoyin lafiya a Makka da Madina.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.