Bayan Dakatar da USAID, An Gano Miliyoyin Daloli da Amurka Ta ba Najeriya a 2024

Bayan Dakatar da USAID, An Gano Miliyoyin Daloli da Amurka Ta ba Najeriya a 2024

  • Najeriya ce a matsayi na bakwai cikin jerin ƙasashen da suka fi karɓar tallafin Amurka a 2024, inda ta samu dala miliyan 763 daga USAID
  • USAID ta raba tallafin zuwa manyan fannoni biyar: lafiya, tsaro, tattalin arziƙi da mulki, abinci, da ilimi wanda ko wanne fanni ya samu miliyoyi
  • A 2024, Ukraine ta samu tallafin dala biliyan 6.1, a bayanta sai Isra’ila, Afghanistan, Jordan, Ethiopia, Yemen, Sudan, Kudancin Sudan da Congo

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Najeriya ta kasance a matsayi na bakwai cikin ƙasashen da suka fi karɓar tallafin Amurka a 2024, inda ta samu dala miliyan 763 daga hukumar USAID.

Tallafin ya fi mayar da hankali kan agajin jin ƙai, kula da lafiya, bunƙasa tattalin arziƙi, da kuma yaƙi da ta'addanci.

Rahoto ya bayyana kudaden da Amurka ta ba Najeriya a 2024 ta hannun USAID
A 2024, Amurka ta ba Najeriya tallafin dala miliyan 763 ta hannun USAID. Hoto: @realDonaldTrump, @officialABAT
Asali: Facebook

Rahoton Vangaurd ya ce tallafin dala miliyan 763 da aka ba Najeriya ya nuna karfin matsayinta a Afirka a dangantaka da Amurka.

Kara karanta wannan

A karshe, gwamnati ta fadi sunayen mutane 16 da ke daukar nauyin ta'addanci a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bangarori 4 da ake amfani da tallafin USAID a Najeriya

Rahoton shafin foreignassistance.gov ya nuna cewa, Najeriya na amfani da tallafin da ta samu daga USAID a wasu manyan bangarori biyar:

1. Lafiya da yawan jama'a

Wani babban kaso na tallafin USAID a Najeriya ya tafi ne kan shirye-shiryen kiwon lafiya, musamman hana yaduwar cutar HIV/AIDS a ƙarƙashin shirin PEPFAR, tare da shawo kan masassara, tarin fuka, da lafiyar iyaye mata.

Hakazalika, Najeriya na samun tallafi kan yawan jama'arta daga USAID, wanda ya shafi yaki da mace-macen mata masu juna biyu, da tamowar yara da sauransu.

A wannan bangare, USAID ta ba Najeriya tallafin dala miliyan 370m a 2024.

2. Tsaro da yaƙi da ta'addanci

Duba da matsalar tsaro da Najeriya ke fama da ita daga Boko Haram, ISWAP, da sauran 'yan ta’adda, Amurka ta ba da tallafi wajen inganta tsare-tsaren tsaro, horar da jami'an tsaro, da shirye-shiryen zaman lafiya a yankin Arewa maso Gabas.

Kara karanta wannan

2027: An gano littafin karni na 10 da ya yi hasashen lokacin ƙarshen duniya

3. Ci gaban tattalin arziki da mulki

Tallafin USAID a Najeriya ya kuma shafi shirye-shiryen rage fatara, ayyukan bunƙasa ababen more rayuwa, da ƙarfafa dimokraɗiyya a ƙasar.

Amurka ta ba Najeriya tallafin dala miliyan 6.5 na bunkasa tattali da dala miliyan 7.9 na karfafa mulkin dimokuradiyya, sannan ta ba da dala miliyan 36 na gudanarwar gwamnati.

4. Abinci da agajin gaggawa

USAID ta bayar da tallafi ga 'yan gudun hijira da dama, musamman a yankunan da rikice-rikicen tsaro suka shafa, inda aka samar da abinci da ruwan sha mai tsafta.

A bangaren shirye-shiryenta na noma, USAID ta ba Najeriya tallafin dala miliyan 7.9 yayin da agajin gaggawa da jin kai ya samu dala miliyan 310.

5. Ilimi da sauransu

USAID ta ba Najeriya tallafin dala miliyan 24 domin bunkasa fannin iliminta musamman a shirye-shiryen ilimin 'ya'ya mata.

Wasu bangarorin da ba a ambata ba, sun lakume dala miliyan 6.3. Wanda ya kai jimillar kudin da Najeriya ta samu zuwa dala miliyan 763 daga USAID a 2024

Kara karanta wannan

Yadda Biden da Amurka su ka matsawa Najeriya lamba, aka saki jami'in Binance

Matsayin Najeriya a kasashe masu karbar tallafin Amurka

Shirin tallafin USAID a kasashen Afrika
Shirin tallafin USAID a kasashen Afrika. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

A cikin 2024, Ukraine ce ta fi karɓar tallafin Amurka, ta samu dala biliyan $6.1, sakamakon yaƙinta da Rasha. Wasu ƙasashe da suka amfana da tallafin sun haɗa da:

  • Isra’ila
  • Afghanistan
  • Jordan
  • Ethiopia
  • Yemen
  • Najeriya
  • Sudan
  • Kudancin Sudan
  • Congo

Trump ya dakatar da tallafin kasashen waje

A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnatin shugaba Donald Trump ta sanar da dakatar da yawancin shirye-shiryen tallafin ƙasashen waje na tsawon kwanaki 90.

Wannan dakatarwar, ta shafi rufe ayyukan hukumar USAID tare da toshe dukkanin tallafin da Amurka ta ke ba kasashe ciki har da Najeriya, wanda ya shafi shirin yaki da HIV/AIDS.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.