Bill Gates Ya Yi Murabus Daga Kamfanin Microsoft Saboda Zargin Alaka da Ma'aikaciyarsa

Bill Gates Ya Yi Murabus Daga Kamfanin Microsoft Saboda Zargin Alaka da Ma'aikaciyarsa

- Rahotanni sun bayyana cewa, Bill Gates ya yi murabus daga shugabancin kamfanin Microsoft

- A cewar rahotannin, attajirin ya bar kamfanin ne sakamakon zarginsa da alaka da ma'aikaciyarsa

- Maganar ta fito ne a yayin da Bill da Melinda Gates ke kokarin tabbatar da saki a tsakaninsu

A shekarar da ta gabata lokacin da Bill Gates ya bar shugabancin kamfanin Microsoft, ya ce aikin agaji ne ya sa ya yanke shawarar, amma sabon rahoto na danganta ficewar tashi da wani lamari da ya faru kusan shekaru 20 da suka gabata.

An ce yana karkashin bincike game da lamarin a shekarar 2019, yayin da kwamitin Microsoft ya nemi Gates ya sauka daga shugabancin kamfanin yayin da binciken ke gudana.

Maganar da ake zarginsa dashi ta kasance tare da wata injiniyar kamfanin Microsoft da ba a bayyana sunanta ba, wacce ta bayyana alakarta da shi a wata wasika. Lamarin ya bayyana ne yayin da Gates da matarsa, Melinda, ke fuskantar cuku-cukun saki.

KU KARANTA: Da Duminsa: 'Yan Sanda Sun Ceto Farfesan UNIJOS da Mijinta Daga 'Yan Bindiga

Bill Gates Ya Yi Murabus Daga Kamfanin Microsoft Saboda Zargin Alaka da Ma'aikaciyarsa
Bill Gates Ya Yi Murabus Daga Kamfanin Microsoft Saboda Zargin Alaka da Ma'aikaciyarsa Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Daraktocin ba su ga dacewar ya kasance a shugabancin kamfanin ba a shekarar 2020 yayin da binciken ya kare, wanda kuma shi ne shekarar da Gates ya yi murabus don fuskantar ayyukan agaji.

Amma wata mai magana da yawunsa ta ce attajirin bai yi murabus saboda binciken ba, in ji Reuters.

Ba a bayyana dalilin binciken ba, amma an bayar da rahoton lamarin cikin aminci.

An ruwaito cewa matan da ke aiki a Microsoft da Gidauniyar Bill da Melinda Gates kan sami alheri daga Bill Gates a wasu lokuta. Har yanzu yana kula da gidauniyar.

Ku lura cewa Gates ya bar shugabancin Microsoft kafin a kammala binciken. Sakamakon binciken wanda wata hukumar dokoki ta gudanar ba a sanar da shi ba.

KU KARANTA: Gwamnonin PDP: Muna Son Buhari Ya Amince da Yiwa Kundin Tsarin Mulki Kwaskwarima

A wani labarin, Bill Gates, attajirin duniya kuma wanda ya kafa kamfanin kwamfuta na Microsoft ya sanar da shirinsa na rabuwa da mai dakinsa Belinda.

Bill da Melinda sun sanar da labarin ne a shafukansu na Twitter a ranar Litinin inda suka ce sun dauki wannan matakin ne bayan nazari sosai.

Ma'auratan sun dade suna jagorantar ayyuka da dama na taimakon jama'a a sassan kasashen duniya daban-daban.

Asali: Legit.ng

Online view pixel