Jihohi 10 da suka fi talauci a Najeriya

Jihohi 10 da suka fi talauci a Najeriya

Hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ta yi amfani da wasu abubuwa a matsayin mizanin auna yawan talauci a jihohin Najeriya, inda ta fitar da jerin jihohi da kuma matakin da suke kai a yawan talauci.

Yawancin jihohin Najeriya na fama da talauci ne saboda rashin shugabanci nagari, almundahana da almuubazzaranci da dukiyar gwamnati da sauransu.

Jerin jihohi guda 10 da talauci yafi yawa a sune kamar haka;

1. Sokoto

An bayyana jihar Sokoto a matsayin jihar da tafi kowacce talauci a Najeriya, inda take da kaso 81.2% a sikelin auna talauci. Ana ganin cewa yanayin marar dadi yana hana bakin haure da masu saka hannun jari zuwa jihar Sokoto.

2. Kastina

Katsina jiha ce da ke kuryar yankin arewa maso yamma na Najeriya, kuma ta fada cikin jerin malautan jihohi saboda rashin wasu masana'antu ko bangarori da zasu samar wa da jihar kudin shiga.

3. Adamawa

Tattalin arzikin jihar Adamawa, kamar na wasu jihohin yankin arewa maso gabas, ya samu nakasu sakamakon yawaitar hare-haren mayakan kungiyar Boko Haram, lamarin da yasa jama'a da dama ke nesanta kansu daga jihar saboda dalilan tsaro. Hakan yasa jihar ta samu kaso 74.2% a sikelin auna talauci.

4. Gombe

Kusan matsalar jihar Gombe iri daya ce data jihar Adamawa da sauran wasu jihohin yankin arewa maso gabas. Jihar Gombe ta samu kaso 73.2% a mizanin auna talauci.

5. Jigawa

Jihar Jigawa tana da kaso 72.1% a sikelin auna talauci a jihohin Najeriya. Ana alakanta talaucin da jihar Jigawa ke fama da shi da rashin ilimi na mafi yawan jama'ar jihar da kuma rashin bunkasar tattalin arziki.

DUBA WANNAN: Kasashen nahiyar Afrika biyar da suka fi samun cigaba

6. Plateau

Duk da kasancewarta jiha mai wuraren ban sha'awa da ke jan hankalin masu yawon bude ido, yawan rikicin kabilanci ya durkusar da tattalin arzikinta, lamarin da yasa ta samu kaso 71% a sikelin auna talauci.

7. Ebonyi

Ebonyi ce kadai jihar yankin kudu maso gabas da ta fada sahun matalautan jihohi a Najeriya. Tana da kaso 70.6% a sikelin auna talauci. An alakanta talaucin jihar da karancin masu ilimi da kuma gwamnati marar kyau.

8. Bauchi

Hukumar NBS ta saka Bauchi a cikin jerin jihohin Najeriya matalauta. Kididdiga ta nuna cewa mafi yawan jama'ar jihar basu da abubuwan more rayuwa sannan yakin Boko Haram ya shafi jihar.

9. Kebbi

Jihar Kebbi na da kaso 72% a sikelin auna talauci a tsakanin jihohin Najeriya.

10. Zamfara

Hukumar NBS ta saka jihar Zamfara cikin jerin jihohi matalauta na shekarar 2019, saboda tana da kaso 70.8 a sikelin auna talauci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng