Tallafin USAID: An Tono Bayanai kan Tiriliyoyin da Amurka Ta ba Najeriya a Shekaru 10

Tallafin USAID: An Tono Bayanai kan Tiriliyoyin da Amurka Ta ba Najeriya a Shekaru 10

  • A cikin shekaru 10 da suka gabata, Amurka ta ba Najeriya tallafin ƙasashen waje na dala biliyan 7.8, kamar yadda rahoto ya nuna
  • Tallafin da Najeriya take samu daga kasashen waje musamman daga Amurka ya taka muhimmiyar rawa a ci gabanta kasar
  • Tallafin Amurka ga Najeriya ya fi karkata kan fannonin lafiya, tsaro da ci gaban tattalin arziki don magance matsalolin gaggawa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Tallafin kasashen waje yana taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban Najeriya, inda Amurka ke daya daga cikin manyan masu bayar da tallafi ga kasar.

Najeriya ce kasa mafi yawan jama’a a Afirka kuma ta kasance kasa ta hudu mafi karfin tattalin arziki, tana da muhimmiyar rawa wajen zaman lafiya da ci gaba.

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu (hagu), Shugaban Amurka, Donald Trump (dama).
Rahoto ya yi bayani kan tallafin tiriliyoyin Naira da Amurka ta ba Najeriya a cikin shekaru 10. Hoto: @officialABAT, @realDonaldTrump
Asali: Facebook

Duk da haka, kalubale kamar talauci, rashawa, da matsalar tsaro sun tilastawa Najeriya ci gaba da neman tallafi daga kasashen waje, inji rahoton Business Insider.

Kara karanta wannan

Majalisa ta amince gwamna Abba Kabir Yusuf ya kafa hukumar tsaro mallakin Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A tsawon shekaru, tallafin Amurka ya fi mayar da hankali kan bangarorin lafiya, tsaro, da ci gaban tattalin arziki don magance bukatun gaggawa da na dogon zango a Najeriya.

Tallafin Amurka ga Najeriya ta fuskar tsaro da lafiya

Daya daga cikin manyan bangarorin tallafin Amurka ga Najeriya shi ne fannin kiwon lafiya, inda aka kashe makudan kudade wajen yaki da cututtuka kamar HIV/AIDS, zazzabin cizon sauro da tarin fuka.

Ta hanyar shirin PEPFAR, Amurka ta ba wa miliyoyin ‘yan Najeriya magungunan rage karfin cutar HIV/AIDS don ceton rayukansu.

Tallafin tsaro shima muhimmin bangare ne na tallafin Amurka, musamman don taimakawa wajen yaki da Boko Haram da sauran kungiyoyin ‘yan ta’adda.

Shirye-shiryen Amurka kamar shirin yakar matsalar tsaro na Trans-Sahara (TSCTP) suna taimaka wa Najeriya wajen yaki da matsalolin tsaro da tabbatar da zaman lafiya.

Kara karanta wannan

'Za mu iya': Tinubu ya dauki mataki da Amurka ta janye tallafin yaki da cutar HIV

Amurka ta tallafawa manoman Najeriya

Baya ga lafiya da tsaro, Amurka na taimakawa wajen bunkasa tattalin arziki ta hanyar shirye-shiryen cigaban noma da farfado da kasuwanci.

Bangaren noma na daya daga cikin manyan bangarorin tattalin arziki a Najeriya, inda Amurka ke tallafawa manoman kasar ta fuskar ba da horo da tallafin kudi.

A cikin shekarun goma da suka gabata, Amurka ta bayar da dala biliyan 7.8 a matsayin tallafin kasashen waje ga Najeriya, kamar yadda bayanan US-FA suka tabbatar.

Legit Hausa ta jero tallafin kudi da Amurka ta ba Najeriya daga shekarar 2015 zuwa 2024.

ShekaraTallafin Amurka ga Najeriya
2015 $446m
2016 $543m
2017 $643m
2018 $877m
2019 $761m
2020 $880m
2021 $922m
2022 $974m
2023 $1b
2024 $783m

Amurka ta toshe tallafin lafiya ga Najeriya

Kara karanta wannan

Gwamnatin Jigawa ta ware wa 'yan majalisa N30bn don yaki da talauci

A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnatin Amurka ta dakatar da tallafin PEPFAR na magance cutar HIV a Najeriya da wasu kasashe masu tasowa.

Dakatarwar ta biyo bayan wata doka da tsohon shugaban Amurka, Donald Trump, ya kawo a lokacin da ya hau kan mulki.

Wannan matakin na Trump na iya kawo cikas ga yaki da cutar HIV a Najeriya, inda miliyoyin mutane ke fama da cutar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.