Babban Attajiri Femi Otedola Ya Samar da Kudin Gina Matatar Dangote? Gaskiya Ta Fito
- An yada wasu rahotanni masu ikirarin cewa hamshakin attajiri, Femi Otedola, ya taimaka da kudi wajen gina matatar Dangote
- Femi Otedola ya fito ya yi martani kan wadannan rahotannin inda ya bayyana cewa akwai abin da ake son cimmawa shiyasa ake yada su
- Hamshakin attajirin ya nuna akwai abin da yake son samu daga wajen matatar ta abokinsa da suka dade suna tare
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Legas - Shahararren attajiri, Femi Otedola, ya yi martani kan rahotannin da ke cewa ya samar da kudade domin gina matatar Dangote.
Femi Otedola ya yi watsi da rahotannin da ke iƙirarin cewa shi ne ya tallafa wa matatar man Dangote da kuɗaɗe, inda ya bayyana rahotannin a matsayin “ƙarya tsagwaronta”.

Source: UGC
Hakan na kunshe ne a wani saƙo Femi Otedola ya wallafa a shafinsa na X ranar Litinin, 4 ga watan Mayun 2026.
Shin Otedola ya sa kudi a matatar Dangote?
Hamshaƙin attajirin ya ce bai saka “kobo ɗaya” a matatar man ba, wadda Aliko Dangote, babban mai masana’antu mafi arziki a Afirka, ya mallaka.
“Rahotannin da ke iƙirarin cewa Femi Otedola ne ya tallafa wa matatar man Dangote da kuɗaɗe ƙarya ne tsagwaronta.
“Ban saka ko kobo ɗaya ba, ko dala ɗaya, ko naira ɗaya.”
- Femi Otedola
Otedola na son sayen hannun jari
Femi Otedola ya bayyana cewa saɓanin waɗannan iƙirarin, shi dai kawai ya nuna sha’awar shiga cikin shirin sayar da hannun jari ga jama’a na matatar man da za a yi nan gaba.
“Ainihin gaskiyar maganar, wadda waɗanda ke yaɗa waɗannan ƙaryar suka yi banza da ita, ita ce Otedola ma buƙatar kaso na musamman yake yi domin ya samu damar shiga cikin shirin sayar da hannun jarin matatar da za a yi nan gaba."
- Femi Otedola
Shin Dangote ya nemi tallafin kudi?
Ɗan kasuwar ya kuma yi watsi da rahotannin da ke nuna cewa Tony Elumelu, shugaban bankin UBA, da Mike Adenuga, shugaban rukunin kamfanonin Globacom, suna da hannu wajen samar da kuɗaɗen gudanar da aikin.
Ya ce Dangote bai taɓa neman tallafin kuɗi daga gare shi ko daga sauran ’yan kasuwar ba, inda ya siffanta iƙirarin a matsayin wani yunƙuri na ganganci don ƙoƙarin raba kan shugabannin ɓangaren kasuwanci masu zaman kansu.
“Zan iya bayyana hakan a sarari cewa babu wani lokaci da Alhaji Dangote ya nemi tallafin kuɗi daga wurin Elumelu, Adenuga da ni kaina."
“Rukunin Kamfanonin Dangote ƙungiya ce tsayayyiya wadda ta ƙware sosai wajen tara manyan kuɗaɗen gudanar da ayyukanta.”
- Femi Otedola

Source: Twitter
Otedola ya bayyana rahotannin a matsayin “makirci da aka tsara” da nufin dasa rashin jituwa a tsakanin ’yan kasuwar Najeriya.
Dangote ya ba surukinsa mukami
A wani labarin kuma, kun ji cewa kamfanin Dangote ya ba da sabon mukami ga surukin Aliko Dangote watau Jamil Mohammed Abubakar.
An naɗa shi a matsayin Manajan darakta na sashen kayayyakin more rayuwa da sufuri na kamfanin inda ake sa ran zai kawo sauye-sauye da dama.
Dangote ya bayyana cewa Jamil Abubakar zai jagoranci ƙoƙarin buɗe sababbin hanyoyin kasuwanci da za su ƙarfafa fitar da kayayyaki da ci gaban masana’antu.
Asali: Legit.ng

