Hukumar USAID ta kaddamar da shirin da zai bunkasa harkar noman masara a Kaduna
- Hukumar USAID ta kafa wani shiri da zai bunkasa harkar noman masara a Kaduna
- Shirn zai tallafawa manoma 20,000 wanda ya kunshi mata a ciki
- Shirin zai taimaka wajen rage talaucin da manoma ke fuskanta
A cikin kokarin inganta harkar noma da take taimakawa wajen tattalin arzikin kasa, hukumar USAID tare da hadin gwiwar kamfanin Nestle na Najeriya sun kaddamar da tsarin ‘Ciyar da Najeriya a gaba da samar da ingatacciyar masarar Nestle' a jihar Kaduna.
Sunan mai taken 'samar da ciyarwa a gaba' na gwamnatin Amirka ne na yaki da cutar yunwa da samar da tsaro a duniya.
Domin kalubalen da ake fuskanta wajen noman masara da rashin samin riba musamman a noman masara da waken soya, hukumar USAID, kamfanin Nestle tare da hadin gwiwar wasu kamfanonin suka kafa wannan shiri.
Shirin zai samar da horo ga manoma, da kananan ma’aikatan noma a jihar Kaduna, manoman zasu koyi yadda za a rage gurbatattun iri don samin bunkasa a masara da waken soya ingatattu wanda zai samar da lafiya ingatacciya a cikin al’umma.
Shirin zai kuma taimakawa manoma sama da 20,000 wanda ya kunshi mata da yawa da masu sana’a a jihar.
DUBA WANNAN: Wata cikin 'yan Chibok da aka ceto daga Boko Haram ta zayyana sirrin kungiyar dalla-dalla
Darakta na hukumar USAID, Stephen Haykin ya bada sanarwar yadda shirin zai tallafawa kananan manoma da fitar da su daga kangin talauci
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng