2027: An Gano Littafin Karni na 10 da Ya Yi Hasashen Lokacin Ƙarshen Duniya
- An gano wani littafi mai shekaru 900 wanda ya yi hasashen cewa ranar kiyama za ta zo nan da shekaru biyu masu zuwa, watau 2027
- Littafin, mai dauke da rubutun wani waliyyin Katolika, Saint Malachy ya yi bayani dalla dalla a kan shugabancin Fafaroma har zuwa na yau
- Ana ganin yakin da ake fama da shi a duniya da rashin lafiyar Fafaroma Francis ya kara maida hankulan jama'a kan hasashen tashin duniya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Vatican City – An gano wani tsohon littafi mai shekaru 900 a kundin ajiyar Vatican wanda ya yi hasashen cewa ranar kiyama za ta zo a shekarar 2027.
Wannan hasashe yana cikin littafin Saint Malachy na ƙarni na 12 mai suna Prophecy of the Popes, wanda ke dauke da jerin jimloli a harshen Latin da ake zaton suna bayani kan kowane Paparoma.

Asali: Getty Images
Jaridar DailyMail UK ta wallafa cewa littafin ya fara da Fafaroma Celestine II a shekarar 1143, kuma ya ƙare da shugaba na yanzu na Cocin Katolika, wato Paparoma Francis.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Littafi kan karshen duniya ya dauki hankali
Legit.ng ta ruwaito cewa an gano littafin mai dauke da jimloli 112 a shekarar 1595 ta hannun wani Arnold Wion, wanda ya ce ya samo rubuce-rubucen Malachy daga ma'ajiyar Vatican.
A jimlar ƙarshe na littafin, an rubuta:
"A ƙarshen zamanin Cocin Katolika, za a yi mulkin Peter na Roma, wanda zai ci gaba da kula da mabiyansa a cikin wahalhalu masu yawa, sannan birnin mai tudu bakwai zai rushe, kuma Babban Alƙali zai yi wa mutane hukunci."
Wasu na fassara wannan hasashe da cewa wani mai suna Peter zai karɓi shugabanci yayin da Paparoma Francis ke fama da rashin lafiya a yanzu.

Asali: Facebook
A gefe guda kuma wasu na ganin hasashen na nufin cewa Francis shi ne Fafaroma na ƙarshe na Cocin Katolika, wanda yanzu haka yana gadon asibiti.
Ana hasashen karshen duniya ya zo
Wani fim ɗin bincike da aka fitar a shekarar 2024 ya nuna cewa hasashen zai cika a 2027, bisa wani bayani da ake dangantawa da Faparoma Sixtus V daga 1585.
Wannan bayani an fassara shi da cewa karshen duniya zai zo bayan shekaru 442 bayan Sixtus V ya hau kan mulki.
Hasashen ya kara daukar hankali a yayin da Faparoma Francis, mai shekaru 88, ya kwanta a asibiti tsawon makonni biyu sakamakon matsalar numfashi.
Ana alakanta yake-yake da karshen duniya
Yakin Ukraine, karin zaman dar-dar tsakanin Amurka da Sin, da rashin kwanciyar hankali a Gabas ta Tsakiya sun kara tada sababbin jita-jita kan wannan hasashe.
Shirin sake kaddamar da makaman nukiliya daga manyan ƙasashe ya kara tayar da fargabar cewa ranar tashin alkiyama ta karato.
An gano sanadin da zai tashi duniya
A baya, mun wallafa cewa binciken kimiyya ya bankado wasu manyan hadurran guda uku da ke barazana ga duniya, wanda aka yi hasashen za su kawo karshen dan Adam a nan kusa.

Kara karanta wannan
An shiga tashin hankali a Bauchi: 'Dan shekara 20 ya kashe mahaifiyarsa da tabarya
A cewar rahoton, akwai bukatar shugabannin duniya su tashi tsaye don magance wadannan barazanar domin kare rayuwar al'umma da kuma tabbatar da zaman lafiya a duniya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng