A karshe, Gwamnati Ta Fadi Sunayen Mutane 16 da Ke Daukar Nauyin Ta'addanci a Najeriya

A karshe, Gwamnati Ta Fadi Sunayen Mutane 16 da Ke Daukar Nauyin Ta'addanci a Najeriya

  • Gwamnatin Najeriya ta ayyana Simon Ekpa, kungiyar Lakurawa da wasu mutum 14 a matsayin masu daukar nauyin ta’addanci
  • An bukaci bankuna da cibiyoyin kasuwanci su toshe duk wasu kudi ko kadarori da ke da alaka da mutanen da aka bayyana a jerin
  • Sunayen da aka fitar sun hada da Ekpa, Godstime Promise Iyare, da wasu kamfanoni kamar Igwe Ka Ala Enterprises da Seficuvi Global

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Gwamnatin tarayya ta ayyana Simon Ekpa da wasu mutane da kamfanoni 15 a matsayin masu daukar nauyin ta’addanci a Najeriya

Haka kuma, gwamnatin ta bayyana ƙungiyar Lakurawa a matsayin ƙungiyar ta’addanci kuma mai daukar nauyin ayyukan ta’addanci.

Gwamnatin tarayya ta fitar da sunayen masu daukar nauyin ta'addanci a Najeriya
Gwamnatin tarayya ta lissafa Simon Ekpa da wasu 15 a matsayin masu daukar nauyin ta'addanci. Hoto: @simon_ekpa
Asali: Twitter

Gwamnati ta ayyana masu daukar nauyin ta'addanci

An dauki wannan mataki ne bayan da aka zarge su da bayar da tallafi da kudi ga kungiyoyin ta’addanci a Najeriya, inji rahoton The Cable.

Kara karanta wannan

Ajali ya yi kira: Hatsabibin ɗan bindiga, Shekau ya mutu yayin arangama da ƴan ta'adda

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An bayyana hakan a wata sanarwa da aka fitar a ranar Alhamis, 6 ga Maris, 2025, bayan da kwamitin sanya takunkumi na Najeriya (NSC) ya bayar da shawarar yin hakan.

Shugaban NSC, wanda shi ne Antoni Janar na tarayya, ya bada umarnin sanya sunan Simon Ekpa da sauran mutanen a cikin jerin masu daukar nauyin ta’addanci.

Wata takarda da aka samo daga kwamitin ta nuna cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya amince da wannan mataki bisa shawarar Antoni Janar na tarayya.

A cewar kwamitin, an gudanar da taro a ranar 6 ga Maris, 2024, inda aka amince da sanya wasu mutane da kungiyoyi a jerin masu daukar nauyin ta’addanci.

Gwamnati ta toshe hanyoyin kudin 'yan ta'addan

Gwamnati ta ce an dauki wannan mataki ne bisa tanadin sashe na 54 na dokar hana ta’addanci ta 2022.

Kara karanta wannan

Sojojin sama sun dura Zamfara, sun dauki alhakin kai harin da ya kashe mutane 11

Saboda haka, an tilastawa duk cibiyoyin hada-hadar kudi da kasuwanci su toshe duk wasu kudi ko kadarorin da ke da alaka da wadannan mutane ba tare da bata lokaci ba.

Haka kuma, dole ne su kai rahoton irin wadannan kadarori zuwa ga sakatariyar kwamitin sanya takunkumi na Najeriya da ke Abuja.

Bugu da kari, gwamnati ta ce dole ne a sanar da hukumar binciken kudin Najeriya (NFIU) duk wata huldar dukiya da ke da nasaba da wadannan mutane.

Gwamnati ta gargadi cibiyoyin hada-hadar kudi da kamfanoni da cewa rashin bin wannan umarni na iya jawo hukuncin doka da kuma bacin suna.

Sunayen masu daukar nauyin ta'addanci a Najeriya

Simon Ekpa ya shiga jerin masu daukar nauyin ta'addanci a Najeriya
Jagoran masu fafutukar kafa kasar Biafra, Simon Ekpa ya shiga jerin masu daukar nauyin ta'addanci. Hoto: @simon_ekpa
Asali: UGC

Rahoton jaridar Punch, ya nuna cewa, gwamnatin tarayyar ta fitar da sunayen mutum 16 da ke daukar nauyin ta'addanci kamar haka:

  1. Simon Ekpa
  2. Godstime Promise Iyare
  3. Francis Mmaduabuchi
  4. John Onwumere
  5. Chikwuka Eze
  6. Edwin Chukwuedo
  7. Chinwendu Owoh
  8. Ginika Orji
  9. Awo Uchechukwu
  10. Nwaobi Henry
  11. Eze Chibuike Okpoto
  12. Ohagwu Nneka Juliana
  13. Mercy Ebere Ifeoma Ali
  14. Igwe Ka Ala Enterprises
  15. Seficuvi Global Company
  16. Kungiyar Lakurawa

Kara karanta wannan

Neman lalata: Majalisa ta yi watsi da bukatar Natasha kan zargin Akpabio

Gwamnati ta bukaci bankuna da cibiyoyin hada-hadar kudi su cigaba da sa ido kan duk wata hulda da wadannan mutane tare da kai rahoto.

Gwamnatin Najeriya ta jaddada kudirinta na yaki da ta’addanci tare da daukar matakin doka kan duk masu daukar nauyin kungiyoyin ta’addanci.

Abin da gwamnatin Najeriya ta kudurta

Gwamnati ta jaddada kudirinta na yaki da ta’addanci tare da gargadin bankuna da kasuwanci cewa rashin bin dokokin hana daukar nauyin ta’addanci zai jawo hukunci.

Wannan mataki na nufin dakile hanyoyin samun kudade ga kungiyoyin ta’addanci tare da tabbatar da tsaron kasa.

Wadannan matakai sun nuna yadda gwamnatin Najeriya ke kokarin dakile ayyukan ta'addanci da kuma toshe hanyoyin samun kudaden da ke tallafawa irin wadannan kungiyoyi.

Haka kuma, an nuna cewa za a dauki matakin doka kan duk wanda ya shiga ko goyi bayan ayyukan kungiyoyin ta'addanci, a ko wace hanya.

Jami'an tsaro sun cafke Simon Ekpa

Kara karanta wannan

Kamfanoni 8 na neman durkusa kasafin 2025, sun ki biyan gwamnati bashin N9.4tn

A wani labarin, mun ruwaito cewa, hukumomin Finland sun kama jagoran 'yan aware masu fafutukar kafa kasar Biyafara a Kudancin Najeriya.

Rahotanni sun nuna cewa bayan gurfanar da Simon Ekpa a kotu, an tasa keyarsa zuwa kurkuku bisa zargin jagorantar ayyukan ta’addanci a Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Salisu Ibrahim ya fadada wannan labari ta hanyar kara bayani kan matakin da gwamnatin Najeriya ke dauka.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng