Masu Garkuwa Sun Yi Amfani da Jirgin Sama wajen Satar Mutum a Kano

Masu Garkuwa Sun Yi Amfani da Jirgin Sama wajen Satar Mutum a Kano

  • Rahotanni sun nuna cewa 'yan sanda sun cafke wasu 'yan kasashen waje biyu da ake zargi da garkuwa da mutane a jihar Legas
  • Bayanin 'yan sanda ya nuna cewa an kama su ne bayan sun yi garkuwa da wani dan kasar Pakistan mai shekaru 48 a yankin Ikeja
  • A yanzu haka, rundunar 'yan sanda ta tabbatar da ana kokarin cafke ragowar mutane biyar da suka tsere bayan aikata laifin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Lagos - Rundunar 'yan sandan jihar Legas ta cafke wasu mutane biyu 'yan asalin kasar Pakistan da ake zargi da aikata garkuwa da mutane a jihar.

Ana zargin mutanen ne da yin garkuwa da wani dan kasar Pakistan da suka janyo daga Kano zuwa Legas bisa alkawarin samun aiki.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun yi magana kan kasuwar sayar da sassan jikin dan Adam

Yan sanda
An kama masu garkuwa daga kasashen waje. Hoto: Nigeria Police
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa an cafke su ne yayin da 'yan sanda ke kokarin kubutar da wanda aka yi garkuwa da shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kakakin rundunar, CSP Benjamin Hundeyin, ya bayyana cewa an kama mutanen ne bayan samun kiran gaggawa a ofishin 'yan sanda na Ikeja a ranar Laraba, 5 ga watan Maris, 2025.

A cewar Hundeyin, bincike ya nuna cewa mutanen bakwai ne suka janyo wanda aka sace zuwa Legas, suka kama shi, suka daure shi sannan suka bukaci a biya kudin fansa har N50m

Yadda aka kama masu garkuwa da mutane

Bayan samun kiran gaggawa daga wani mutum a Kano, rundunar 'yan sanda ta Legas ta tura jami'anta cikin gaggawa don kubutar da wanda aka yi garkuwa da shi.

A yayin aiki, 'yan sanda sun samu nasarar kama mutane biyu daga cikin wadanda ake zargi da aikata laifin.

Kara karanta wannan

Yadda sufetan 'dan sanda da matasa suka lakadawa tsinannen duka ya rasu a Jos

An bayyana sunayensu da Roman Gull mai shekaru 19 da kuma Aftab Ahmad mai shekaru 28. Sauran mutane biyar sun tsere yayin da ake kokarin cafke su.

Masu garkuwa sun yi amfani da jirgi

PM News ta bayyana cewa wanda aka yi garkuwa da shi an yaudare shi da cewa zai samu aikin girki a Legas.

Wadanda suka aikata laifin sun biya masa kudin jirgi daga Kano zuwa Legas sannan suka sauke shi a wani otel a ranar 28 ga Fabrairu, 2025.

A rana ta gaba, mutane bakwai suka je wurinsa, suka daure shi sannan suka tura sakon neman kudin fansa ga mai gidansa a Kano, suna barazanar kashe shi idan ba a biya N50m ba.

Kayayyakin da aka samu wajensu

A yayin da aka kama wadanda ake zargi, an samu wasu muhimman abubuwa a hannunsu da suka hada da kudin Dala $2,000, katunan ATM guda uku.

Kara karanta wannan

'Dan bindiga ya tono sirrin 'yan ta'adda ga sojoji kafin 'yan uwasa su harbe shi

Haka zalika an samu katin izinin zama a kasar waje lasisin tuki da katin zama dan kasa na NIN a wajensu.

Kakakin rundunar 'yan sanda ya tabbatar da cewa ana ci gaba da kokarin kamo sauran mutane biyar da suka tsere domin su fuskanci shari’a.

Ya ce da zarar an kammala bincike, za a gurfanar da wadanda aka kama a kotu domin fuskantar hukunci.

Sojoji
Hafsun tsaro, Janar Musa. Hoto: Defence Headquarters
Asali: Facebook

An rusa gidajen masu garkuwa a Edo

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Edo ta ruguza wani gida da ake zargin na masu garkuwa da mutane.

Rahotani sun tabbatar da cewa an kama mutane biyu da ke da alaka da gidajen kuma sun bayyana yadda suke sace mutane.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng