Sani Hamza
5185 articles published since 01 Nuw 2023
5185 articles published since 01 Nuw 2023
Rikici ya barke tsakanin ’yan sanda da sojojin sama a Delta kan sakin wanda ake zargi da safarar miyagun kwayoyi. Ana binciken lamarin don shawo kan matsalar.
Mawakin Najeriya, 2Baba ya nemi auren 'yar majalisar Edo, Natasha Osawaru, ya kuma musanta cewa tana da hannu a matsalolin aurensa da Annie Idibia.
An samu matsala a tushen wuta naƙasa, wanda ya janyo daukewar wuta a yankunan Abuja, Kogi, Neja da Nasarawa. Ana kan aikin gyara tare da hukumomi.
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya karbi shugabannin NNPP da suka koma APC saboda rashin tabbas da manufofin Kwankwasiyya marasa amfani.
Mawaki 2Baba ya sanar da soyayyarsa ga Natasha Osawaru, ‘yar majalisar Edo, kwanaki 16 bayan rabuwarsa da Annie, yana mai cewa zai aure ta nan gaba.
Al’ummar Kuryar Madaro da ke Zamfara sun koka kan sabon sansanin ɗan ta'adda, Dan Sa’adi da ke kai hare-hare. Sun nemi karin matakan tsaro daga gwamnati.
Wata daliba a Jami’ar UNIZIK ta ciji malami bayan sun samu sabani kan daukar bidiyon TikTok. Jami’an tsaro sun fara bincike kan don gano gaskiyar lamarin.
Matatar Dangote ta rage farashin dizal zuwa N1,020 daga N1,075, domin taimakawa masana’antu da ‘yan Najeriya wajen rage tsadar rayuwa da bunkasa tattalin arziki.
Kwamitin majalisar dattawa ya binciki Sufeto-Janar kan bacewar bindigogi 178,459, ciki har da bindigar AK-47 guda 88,078, yana mai kira a gano inda suka ke.
Sani Hamza
Samu kari