A Hukumance, Gwamnan Akwa Ibom Ya Bayyana Kudirinsa na Ficewa daga Jam'iyyar PDP

A Hukumance, Gwamnan Akwa Ibom Ya Bayyana Kudirinsa na Ficewa daga Jam'iyyar PDP

  • Gwamna Umo Eno ya bayyana aniyarsa ta ficewa daga PDP saboda rikicin shugabanci da ke damun jam’iyyar a matakin ƙasa
  • Ya ce duk da cewa ya ci zabe a 2023 karkashin PDP, yanzu jam’iyyar ba ta da tsari mai ɗorewa da zai tabbatar masa da nasararsa a 2027
  • Gwamnan jihar na Akwa Ibom ya bukaci dukkanin kwamishinoni da masu rike da mukami su biyo shi zuwa jam'iyyar APC ko su murabus

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Akwa Ibom – Gwamnan jihar Akwa Ibom, Umo Eno, ya sanar da aniyarsa ta ficewa daga jam’iyyar PDP da aka zabe sa cikinta a hukumance.

Da yake jawabi a taron majalisar zartarwar jihar a ranar Alhamis, Eno ya bayyana rikice-rikicen cikin gida da ke damun PDP a matsayin dalilinsa na son barin jam'iyyar.

Gwamnan jihar Akwa Ibom ya bayyana kudurinsa na fiewa daga jam'iyyar PDP
Gwamnan jihar Akwa Ibom, Pastor Umo Eno. Hoto: @_PastorUmoEno
Asali: Twitter

Dalilin Gwamna Eno na son barin PDP

A wani bidiyo da Channels Television ta wallafa, gwamnan ya ce yana son PDP, amma dole zai hakura ya bar ta saboda rikicin shugabanci da ke addabar jam’iyyar a matakin ƙasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar Gwamna Umo Eno:

“Ina son PDP, kuma ina son in zauna a cikin PDP, amma gaskiya babu wani sahihin tsarin da zai tabbatar da cewa zan iya samun kwanciyar hankali a lokacin zaɓe, ba don ba za mu ci zaɓe ba.
“A halin da ake ciki a wannan jiha, da aikin da muka yi gaba ɗaya, ko da mun tsaya takara a ƙarƙashin jam’iyya mara suna, za mu ci zaɓe.
"Amma muna sane da cewa a matakin ƙasa jam’iyyarmu ba ta da haɗin kai, wannan babbar barazana ce a gare mu.”

Gwamna Eno ya fadi matsalolin PDP

Gwamna Eno ya yi gargadin cewa rikicin shugabanci da ke addabar PDP a matakin kasa na iya janyo wa su fadi a zaɓe ta hanyar “kuskuren doka.”

“Kullum ana maganar sakatare wannan da wancan; kai ne za ka ɗauki fom ɗinka ka kai masu, su aika shi zuwa INEC, za ka shiga zaɓe, maimakon a tabbatar da nasararka, sai a ce ka rasa komai saboda wanda bai dace ba ne ya sanya hannu a takardar."

- Gwamna Umo Eno.

A cikin watannin baya, gwamnan jihar na Akwa Ibom ya rika nuna alamun cewa yana shirin barin PDP domin komawa jam’iyyar APC mai mulki, inji rahoton The Cable.

Gwamnan jihar Akwa Ibom ya ce rikicin da ya mamaye PDP ne ya sa shi son barin jam'iyyar
Gwamnan jihar Akwa Ibom, Pastor Umo Eno. Hoto: @_PastorUmoEno
Asali: Twitter

'Ku bi ni zuwa APC ko ku ajiye aiki' - Uno

Mun ruwaito cewa Gwamna Eno ya bukaci dukkanin kwamishinoninsa da sauran masu rike da mukaman siyasa a jihar da su bi shi zuwa APC ko su ajiye aikinsu.

Gwamnan ya ce duk wanda ke da ra’ayin ci gaba da zama a PDP yana da ‘yanci, amma ba zai ci gaba da kasancewa a cikin majalisar zartarwarsa ba.

“Ba sabon abu ba ne cewa zan bar jam’iyyar PDP
“Na ji wasu daga cikinku na cewa ba za ku biyo ni ba. Kuna da ‘yancin yin haka, amma ba za ku ci gaba da zama a majalisar zartarwa ta jiha ba.
"Don haka, ku shirya murabus ranar da na sanar da ficewata, domin ni ne na baku aiki kuma dole ne in samu cikakkiyar biyayya daga gare ku."

- Gwamna Umo Eno.

Kwamishinonin Akwa Ibom sun fusata Gwamna Eno

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Gwamna Umo Eno na jihar Akwa Ibom ya bayyana fushinsa kan yadda wasu kwamishinoni ke barin wurin taro kafin shi ya bar wajen.

Ya jaddada cewa dole ne kowane kwamishina ya kasance tare da shi har zuwa ƙarshen kowane taro, yana mai cewa wajibi ne su tabbatar da dawowarsa gida ko ofis kafin su watse.

A baya, gwamnan ya ya yi wa fiye da mutum 200 daga cikin mukarrabansa gargaɗi bisa rashin halartar wani muhimmin taro da aka shirya a jihar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.