Ana Shirin Nada Sabon Sarki, Mutane Sun Barke da Ihun "Tinubu Zai Sha Kasa a 2027"

Ana Shirin Nada Sabon Sarki, Mutane Sun Barke da Ihun "Tinubu Zai Sha Kasa a 2027"

  • Tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya gana da Rauf Aregbesola a wani yunkurin kafa kawancen adawa gabanin 2027
  • A cikin bidiyon da Atiku ya wallafa, an ji wasu daga cikin mutanen Aregbesola suna rera wakar “Tinubu zai sha kasa a 2027”
  • An rahoto cewa Atiku Abubakar ya gana da tsohon gwamnan na jihar Osun ne jim kadan kafin nadin sabon sarkin Ijesaland na 49

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Osun – Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, kuma dan takarar shugaban kasa a 2023, Atiku Abubakar, ya gana da tsohon gwamnan jihar Osun, Rauf Aregbesola.

An rahoto cewa ganawar da ta gudana a Ilesa, jihar Osun a ranar Juma'a, wani yunkuri ne da ke da alaka da kafa kawancen jam’iyyun adawa gabanin zaɓen 2027.

Mutanen Aregbesola sun tarbi Atiku da wakar "Tinubu zai sha kasa a 2027."
Shugaba Bola Tinubu ya hadu da Atiku Abubakar. Hoto: @PBATMediaCentre
Asali: Twitter

"Tinubu zai sha kasa a 2027" - Mutanen Osun

A wani bidiyo da Atiku ya wallafa a shafinsa na X, an ga lokacin da ya isa gidan Aregbesola da ke Ilesa, tare da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Namadi Sambo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Atiku ya rubuta cewa:

“Lokacin karin kumallo a gidan tsohon gwamnan jihar Osun, Injiniya Rauf Aregbesola.”

A cikin bidiyon, an ji wasu daga cikin mutanen Aregbesola suna rera wakar “Tinubu zai sha kasa a 2027”, yayin da Atiku da Sambo ke mika gaisuwa ga tsohon ministan harkokin cikin gida.

Fitattun ‘yan siyasar Osun da suka tarbi Atiku da tawagarsa sun haɗa da tsohon shugaban jam’iyyar APC a jihar Osun, Lowo Adebiyi, inji rahoton The Guardian.

Sauran sun hada da shugaban ƙungiyar Omoluabi Progressives, Alhaji Azeez Adesiji; tsohon sakataren gwamnatin jihar, Moshood Adeoti; da tsohon kakakin majalisar jihar, Najeem Salaam.

Za a nada sabon sarkin Ijesaland

Ziyarar Atiku na zuwa ne awanni kaɗan kafin bikin nadin sabon sarkin Ijesaland na 49, Oba Clement Adesuyi Haastrup, da aka shirya gudanarwa a Ilesa, Osun.

Wata babbar kotun jihar Osun da ke zama a Ilesa ta ƙi amincewa da dakatar da bikin nadin sarautar, wanda aka shirya yi a dakin taro na Obokungbusi da kuma liyafa a makarantar Ilesa.

Tinubu ya gana da tsohon gwamnan Osun yayin da aka tattaunawa kan kawancen adawa
Atiku Abubakar ya hadu da Olusegun Obasanjo da gwamnan Osun a bikin nadin sabon sarki. Hoto: @atiku
Asali: Twitter

Atiku ya tabbatar da magance kawance

A wani labari mai nasaba da haka, kakakin Atiku, Paul Ibe, ya bayyana cewa Atiku da wasu manyan ‘yan siyasa na ci gaba da tattaunawa kan kafa kawancen adawa da zai fuskanci shugaba Bola Tinubu da jam’iyyar APC a 2027.

Paul Ibe ya ce:

“Kamar yadda kowa ya sani, akwai tattaunawa tsakanin Atiku Abubakar da wasu jagororin adawa irinsu: Peter Obi, Nasir El-Rufai da sauransu.”

Ya ƙara da cewa:

“Tattaunawar na ci gaba, kuma a ƙarshe za a fito da matsaya bisa ra’ayoyi da muradun ‘yan Najeriya.”

Kalli dandazon mutanen da suka tarbi Atiku a gidan Aregbesola a nan kasa:

Ibrahim Shekarau ya shiga hadakarsu Atiku

A wani labarin, mun ruwaito cewa, tsohon gwamnan Kano, Mallam Ibrahim Shekarau, ya shiga cikin sabuwar hadakar manyan 'yan adawar Najeriya.

A yayin wani taron kwamitin hadakar da aka gudanar a ranar Alhamis, an tsayar da ranar 30 ga Mayu 2025 domin yanke hukunci kan ko za a kafa sabuwar jam’iyya ko kuma a shiga wata.

Tsohon gwamnan Rivers, Rotimi Amaechi, na jagorantar kwamitin da ke duba yiwuwar kafa sabuwar jam’iyyar adawa, yayin da suke nazari kan yiwuwar shiga SDP ko ADC.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.