Muhammad Malumfashi
19736 articles published since 15 Yun 2016
19736 articles published since 15 Yun 2016
Gwamnan CBN, Folashodun Shonubi ya shaida cewa marasa gaskiya ne su ka shiga harkar canji, hakan ya jawo Dalar Amurka ta ke cigaba da hawa kan Naira a kasuwa.
Kungiyar ECOWAS ta nuna da gaske za ta yaki Nijar a kan juyin mulkin da aka yi. Idan har makwabta suka shigowa Nijar, za a rasa Shugaba Mohamed Bazoum a Nijar.
Malam Muhammadu Sanusi ya yi wa ‘yan jarida jawabi bayan zamansa da Bola Ahmed Tinubu, a cewarsa dole sai an samu mafitar da za tayi wa Nijar da Najeriya aiki
A yanzu rokon Allah (SWT) ne kadai zai iya rike Dalar Amurka. Mutane su na neman Dalar Amurka ido rufe amma babu isassun kudi bayan kawo sabon tsarin nan CBN.
Tsohon Kwamishinan Kano ya zama babban Hadimin Abdullahi Umar Ganduje a Sakatariyar APC. Malam Muhammad Garba ya zama shugaban ma’aikata watau COS a APC ta kasa
Ministoci biyar kacal za a nada daga Kudu maso gabas, alhali an warewa sauran yankuna kujeru da-dama. ‘Yan Majalisa su na so a kara yawan Ministoci zuwa 50.
Farfesa Tahir Mamman ya taba zama malamin Sanata Kaka Shehu Lawan a jami’ar UNIMAID. Tsohon dalibinsa ne wanda ya taimaka masa wajen ganin ya zama Minista.
A sakamakon mukami da karin wahala da aka ba Hon. Hajara Wanka ta jefa kafa daya a cikin ofishin Kwamishina a jihar Bauchi, ta bar Majalisar NWC a PDP a .Bauchi
A yau Sarkin Kano na 14, kuma Halifan darikar Tijjaniyyah na Najeriya, Muhammadu Sanusi II, ya samu ganawa da Shugaban mulkin sojan Nijar, Abdulrahmane Tchiani.
Muhammad Malumfashi
Samu kari