China Ta Dura kan Amurka, Ta Yi Magana Mai Zafi kan Zargin Tura Makamai zuwa Iran
- Gwamnatin kasar China ta musanta rahoton da ake yadawa cewa tana shirin tura karin makamai zuwa kasar Musulunci ta Iran
- Ta bayyana zargin a matsayin kirkirarre, tare da gargadin Amurka da kada ta yi amfani da hakan a matsayin hujjar kakaba mata haraji
- Wannan lamari da ya sake tasowa na iya kara dagula alakar kasashen biyu tun kafin ziyarar da ake sa ran Shugaba Trump zai kai China
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
China - Kasar China ta karyata rahotannin da ke cewa tana shirin bai wa Iran makaman kariya daga hare-haren sama domin taimaka mata wajen yakar Amurka da Isra'ila.
China ta kuma yi gargadin cewa za ta dauki matakin martani idan Amurka ta yi amfani da zargin a matsayin hujjar kara haraji kan kayayyakin kasar.

Source: Getty Images
Yadda Amurka ta fara zargin China
Rahoton NBC News ya tattaro cewa wasu bayanai hukumomin leken asirin Amurka sun nuna cewa China na shirin tura sababbin makamani ga Iran a makonni masu zuwa.
Wannan zargi ya sa Shugaban Amurka, Donald Trump ya yi barazanar kakaba karin haraji na kashi 50 cikin dari kan kayayyakin China.
Sai dai Kakakin ma’aikatar harkokin wajen China, Guo Jiakun, ya bayyana a wani taron manema labarai a Beijing cewa rahotannin ba su da tushe balle makama.
China ta musanta tura makamai Iran
Ya ce China na bin ka’idoji masu tsauri wajen fitar da makaman soja, tare da kiyaye dokokinta na cikin gida da kuma dokokin kasa da kasa.
“Rahotannin da ake yadawa (cewa za mu tura wa Iran karin makamai) baki daya kirkirarru ne,” in ji shi.
Jiakun ya jaddada cewa kasar China ba ta karya dokokin kasa da kasa wajen fitar da makamai, tana bin komai bisa tsari.

Kara karanta wannan
Wata sabuwa: Matsalar da aka samu a sulhun Amurka da Iran ya rusa burin 'yan Najeriya
China ta shirya sa kafar wando daya da Amurka
Ya kara da cewa idan Amurka ta nace wajen amfani da wannan zargi a matsayin hujjar kakaba karin haraji, to China ba za ta zuba ido ba, za ta dauki matakan da suka dace domin kare muradunta.
Wannan sabuwar takaddama na zuwa ne gabanin wata ziyarar da ake sa ran Shugaba Trump zai kai China domin ganawa da shugabanta, Xi Jinping, wadda tuni aka jinkirta saboda rikicin Iran.

Source: Getty Images
Kasashen biyu na kokarin farfado da yarjejeniyar kasuwanci mai rauni da ke tsakaninsu, amma wannan sabon rikici na iya kara dagula alakar tattalin arzikin Amurka da China.
Masu sharhi na ganin cewa wannan sabani tsakanin kasashen biyu na iya kara tsananta rikicin kasuwanci a duniya, musamman idan aka ci gaba da daukar matakan ramuwar gayya tsakaninsu.
China ya jaddada goyon bayan Iran
A wani labarin, kun ji cewa China ta sake nuna goyon bayanta ga Iran bayan da Amurka ta sanar da daukar matakin hana jiragen Iran wucewa ta mashigar Hormuz.

Kara karanta wannan
Muhimman abubuwa 5 da Amurka da Iran suka gaza warwarewa a zaman sulhu a Islamabad
Ma’aikatar harkokin waje n China ta ce ƙasarta na goyon bayan Iran wajen kare ikon ƙasarta da kuma muradunta, tana mai jaddada cewa kowace ƙasa na da ‘yancin kare kanta.
Ta kuma yi kira ga Amurka da ta guji tsoma baki cikin al’amuran cikin gida na China ko na Iran , tana mai cewa irin wannan mataki na iya ƙara tayar da hankali a yankin da ma duniya baki ɗaya.
Asali: Legit.ng
