Tsohon Sarkin Kano Sanusi II Ya Zauna Da Sojojin Da Suka Kifar Da Bazoum a Nijar

Tsohon Sarkin Kano Sanusi II Ya Zauna Da Sojojin Da Suka Kifar Da Bazoum a Nijar

  • Muhammadu Sanusi II ya isa Nijar, zai zauna da sojojin da su hambarar da gwamnatin farar hula
  • Tawagar AU da ECOWAS ta gagara shawo kan jagoran sojojin tawaye, Janar Abdulrahmane Tchiani
  • Idan an yi nasara, watakila hakan ziyarar ta kawo sasanci kuma ayi maganin barkewar yaki a nahiyar

Niamey - Mai martaba Khalifa Muhammadu Sanusi II ya sa labule da Shugaban sojojin tawayen Jamhuriyar Nijar, Janar Abdulrahmane Tchiani.

Hotunan da mu ka samu daga kafofin sadarwa na zamani sun tabbatar da cewa Sarkin Kano na 14 ya yi zama da sojojin da su ka karbe iko a Nijar.

Rahoton Aminiya ya nuna an yi taron ne a ranar Laraba a Yamai watau Niamey, babban birnin Nijar a lokacin da abubuwa su ke faman canza zani.

Kara karanta wannan

Nijar Ta Nada Shirgegen Mukami Yayin Da Kasar Ke Cikin Matsin Lamba Na Mika Mulki Daga ECOWAS, Bayanai Sun Fito

Muhammadu Sanusi
Tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi a Nijar Hoto: babarh
Asali: Twitter

Ana sa ran sulhu ya yiwu a Nijar

Kafin wannan zama Janar Abdulrahmane Tchiani ya hadu da wakilan kungiyoyin ECOWAS da AU bayan ya hambarar da Mohammeed Bazoum.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sulhun da kungiyoyin kasashen Yammacin Afrika da ta tarayyar nahiyar su ka nemi yi bai yiwu ba, sannan gwamnatin Amurka ta gaza yin komai.

Baya ga makwabtaka, Najeriya da Nijar su na da kyakkyawar alaka mai tarihi, watakila Muhammadu Sanusi zai yi amfani da wannan dama.

Sanusi II ya na tare da Sarkin Damagaram

Wani matashi mai amfani da shafin Twitter a Najeriya, @babarh_ ya bayyana cewa Sarkin Damagaram ya yi wa Sanusi II iso zuwa fadar a Yamai.

Hotuna da bidiyo sun nuna sarakan za su zanta da sojojin da su ka karbe mulki da karfi da yaji bayan Bazoum ya shafe shekaru ya na kan karaga.

Kara karanta wannan

ECOWAS: Dakarun Mali Da Burkina Faso Sun Isa Jamhuriyar Nijar? Bayanai Sun Fito

Khalifa Sanusi II zai yi nasara?

A matsayinsa na Khalifan darikar tijjaniya, Basarake kuma masanin tattalin arziki, ana girmama Mai martaba Sanusi II sosai a Yammacin Afrika.

Daily Trust ta ce ana tunanin Basaraken ya je Nijar ne domin a sasanta da Janar Janar Tchiani mai shekara 62 domin gudun yaki ya barke a kasar.

Ko a lokacin da aka tsige Sanusi II daga matsayin gwamnan babban bankin Najeriya a 2014, ya na Jamhuriyyar Nijar ne domin halartar wani taro.

Asali: Legit.ng

Online view pixel