Naja’atu Muhammad Ta Tona Abin Da Ya Jawo Shugaba Tinubu Zai ‘Yaki’ Kasar Nijar

Naja’atu Muhammad Ta Tona Abin Da Ya Jawo Shugaba Tinubu Zai ‘Yaki’ Kasar Nijar

  • Hajiya Naja’atu Muhammed tayi kaca-kaca da gwamnatin Bola Tinubu a kan shirin yakar Nijar
  • ‘Yar siyasar ta na ikirarin an dauko batun yakin ne ganin ana shari’a da APC a kotun karar zabe
  • Naja’atu ta ce Tinubu ya san bai ci zabe ba, shiyasa ya ke neman daurin gindin kasashen Duniya

Abuja - Fitacciyar ‘yar siyasa kuma tsohuwar jigo a jam’iyyar APC, Naja’atu Muhammed ta ce barazanar kai wa Nijar hari duk dodorido ce.

Daily Trust ta rahoto Hajiya Naja’atu Muhammed ta na bayanin abin da ta kira dalilin kungiyar ECOWAS da Bola Tinubu na aukawa kasar Nijar da yaki.

Kasashen yammacin Afrika a karkashin jagorancin shugaban Najeriya sun nuna za su yaki Nijar saboda juyin mulki, ‘yar siyasar ta ce ba a nan take ba.

Kara karanta wannan

Gwamnan CBN Ya Fadi Abin Da Ya Jawo Naira Ta Sunkuya War-Was a Kasuwar Canji

Bola Tinubu
Bola Tinubu da ECOWAS za su iya yakar Nijar Hoto: Dolusegun
Asali: Twitter

Shari'ar zaben 2023 a kotu

A cewar Naja’atu Muhammed, buga gangunan yaki, dabara ce da aka kawo domin kawar da tunanin mutane ga abin da ke faruwa a kotun zabe.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Atiku Abubakar da Peter Obi su na karar Bola Tinubu, APC da hukumar INEC kan zaben shugaban kasa, an kusa kammala shari’ar a kotun korafi.

A cewarta, dole kowa ya yi tir da abin da Najeriya ta ke shirin yi, ta ce Faransa ta na tare da Bola Tinubu bayan ya murde zabe wajen hawa mulki.

Ka da mu goyon bayan a tafi yaki

A wani jawabi da ta fitar a jiya, shahararriyar ‘yar siyasar tayi kira ga al’umma su taru wajen hada-kai domin kin goyon bayan ECOWAS ayi yaki.

"Idan aka shiga yaki, Tinubu zai iya kawo dokar ta-baci, ya fito da dokar da za ta halatta masa zama a kan mulki har illa Ma Sha Allahu

Kara karanta wannan

Juyin Mulki: Bidiyo Ya Bayyana Yayin da Asari Dokubo Ya Sha Alwashin Yin Kasa-Kasa Da Gwamnatin Sojan Nijar

A haka sai ayi watsi da kotun zabe ko wata shari’ar da ta ke kalubalantar cancantarsa ko damar shiga takararsa a zaben Najeriya.
Idan ya samu goyon bayan Faransa da sauran manyan Duniya, zai iya baza jami’an tsaro domin ya hana ayi masa duk wani bore.
Tinubu ya san cewa bai cancanci shiga takara ba. Alkalan kotun karar zaben sun san wannan, APC a matsayin jam’iyya ta san haka.
Meyasa Tinubu ya kagara ya shiga yaki a madain Faransa da sunan kare mulkin farar hula?

- Hajiya Naja’atu Muhammed

Man fetur zai kuma tashi

Ku na da labari mai zai kara tsada a Najeriya domin Gwamnati Bola Tinubu ba ta biyan tallafin man fetur, kuma ba a tace danyen mai a Najeriya.

An samu kusan karin 20% a darajar Dala a kasuwar canji, idan aka yi amfani da wannan lissafi, IPMAN ta ce litarman fetur zai zama N750 kenan.

Kara karanta wannan

Sanusi II Ya Yi Maganar Farko Bayan Haduwa da Tinubu da Sojojin Juyin Mulkin Nijar

Asali: Legit.ng

Online view pixel