Bankin CBN Ya Fadi Abin Da Ya Jawo Naira Ta Sunkuya a Kasuwar Canjin Kudi

Bankin CBN Ya Fadi Abin Da Ya Jawo Naira Ta Sunkuya a Kasuwar Canjin Kudi

  • Gwamnan bankin CBN ya yi karin haske a game da abin da ya jawo Naira ta ke karyewa a kasuwa
  • Folashodun Shonubi ya gabatar da lacca a Abuja, ya ce ana zargin Daloli su na shiga hannun ‘yan canji
  • Babban bankin Najeriya ya bayyana yadda marasa gaskiya su ka rungumi harkar canjin kudi a yau

Abuja - Babban bankin Najeriya watau CBN ya ta’allaka faduwar Naira da aiko da kudi da ake yi daga kasashen ketare ba tare da hukuma ta sani ba.

A ranar Alhamis, Daily Trust ta ce Gwamnan bankin CBN na rikon kwarya, Folashodun Shonubi ya yi wannan bayani a makarantar tsaro a Abuja.

Folashodun Shonubi ya gabatar da takarda ga daliban makarantar da ke kwas na EIMC 16 mai taken aiko kudi daga ketare da cigaban tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Chibok: Mai Shekara 13 Da Boko Haram Suka Dauke Ta Dawo Gida Ta Na ‘Yar Shekara 22

Gwamnan Bankin CBN
Gwamnan CBN, Folashodun Shonubi ya fadi dalilin tashin Dala Hoto: @Cenbank
Asali: Twitter

Naira ta sukurkuce a kan Dala

Laccar ta zo ne a lokacin da Dalar Amurka tayi gagarumin tashi, ta kai an saida $1 a kan N950.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A bayanin da Gwamnan babban bankin ya yi, ya nuna marasa gaskiya sun shiga harkar kasuwar canji, su na juya makudan kudi cikin sauki.

Shonubi yake cewa an shigo da makudan Daloli daga kasashen waje ba tare da an san da zamansu ba, a karshe dalolin su ka shiga kasuwar canji.

Jawabin Folashodun Shonubi

“Kudi sun shigo, an samu Daloli, mun san cewa an samu Daloli amma ba mu da labarinsu a hukumance, saboda haka sun shiga kasuwar canji.
Saboda haka dole Daloli su shiga wasu wurare.
Kuma matsalar da ake samu daga kasuwar canji ko duk abin da za ka so ka kira su, shi ne ba a lura da su a sa ido, sun zama kafar aikata laifuffuka.

Kara karanta wannan

Duk Yaudara ce: Naja’atu Ta Tona Dalilin Shugaba Tinubu Na Tsokano ‘Yaki’ Da Nijar

Mu na binciken ma’aikatan banki, ba ‘yan banki kadai ba, duk wani wanda ya aikata laifi, abin da su ke fara yi shi ne su tafi wajen ‘yan kasuwar canji.
Mutane su na so su canza kudinsu zuwa daloli domin ya fi saukin dauka.

- Folashodun Shonubi

'Yan ci-rani su na wayyo Allah

Da mu ka zanta da wani mutumin Najeriya da yake karatu a kasar waje, ya shaida mana su na shan bakar wahala wajen samun kudin ketaren.

Dalibin da yake digir-digir ya ce dole gwamnatin tarayya da ta dauki nauyinsu ta karo masu kudin domin Naira ta karye raga-raga a kasuwa.

Gangar yaki a Afrika

Baya ga tashin Dala, ana da labari kungiyar ECOWAS ta nuna da gaske za ta yaki Nijar a kan juyin mulkin da aka yi a karshen watan Yuli.

Idan kuwa makwabta suka shigowa kasar Nijar da yaki, za a iya rasa Shugaba Mohamed Bazoum domin sojoji na barazanar kashe shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel