An Tafi Kamun Kafa Wajen Ganduje Domin Tinubu Ya Bada Mukamai a Gwamnati

An Tafi Kamun Kafa Wajen Ganduje Domin Tinubu Ya Bada Mukamai a Gwamnati

  • Benjamin Kalu ya kai wa Abdullahi Umar Ganduje ziyara kwanaki da zamansa shugaban APC
  • Mataimakin shugaban majalisar wakilan tarayya ya yi amfani da damar wajen neman alfarma
  • Hon. Kalu ya roki Bola Ahmed Tinubu ya kara yawan kujeru daga Ministocin kudu maso gabas

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Mataimakin shugaban majalisar wakilai, Benjamin Kalu ya yi kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kara masu ministoci.

This Day ta ce Honarabul Benjamin Kalu ya roki Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya taimakawa ‘Yan Kudu maso gabas da karin mukamai.

‘Dan majalisar ya jefa wannan sako zuwa ga fadar shugaban kasa ne a lokacin da ya ziyarci shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje.

Ganduje Shugaban APC
Shugaban APC da Benjamin Kalu Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR
Asali: Facebook

A ranar Alhamis, Kalu ya zauna da Dr Abdullahi Ganduje a sakatariyar jam’iyya mai mulki. Hakan na zuwa bayan ya shiga ofis kwanan nan.

Kara karanta wannan

Ministocin Tinubu: Mutum 5 Da Suka Sha Wahala Kafin a Tantance Su a Majalisa

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

An yi wa Ibo kauron mukamai

Ganin yankin Kudu maso gabas ya samu mafi karancin kujerun ministoci, wasu sun fara kira da a kara masu kujeru kamar sauran yankuna.

Bayan ya gama ganawa da Ganduje, a yayin da yake zantawa da manema labarai a garin Abuja, Kalu ya ce sun cancanci karin wasu ministoci.

Duk da mutanen Kudu maso gabashin kasar ba su zabi jam’iyyar APC sosai a 2023 ba, Kalu ya ce an yi masu sakayya da kujerar da yake kan ta.

‘Dan majalisar na Abia shi ne mataimakin shugaban majalisar wakilan tarayya, a dalilin haka yake kara godewa mai girma shugaban Najeriya.

"Amma kuma mu na kara rokon shi domin shi mutum ne mai alheri, ya duba batun kara kujerun ministoci daga yankin."

Kara karanta wannan

Sanatoci 15 Daga Kudu Sun Taso Shugaban Kasa Ya Kara Masu Ministoci 2

- Ben Kalu

Sun ta ce baya ga rokon mukamai a gwamnatin tarayya, Hon. Kalu ya ce shi da Ganduje sun tattauna kan muhimman abubuwa game da kasar.

Meyasa Tinubu zai yaki Nijar?

Naja'atu Muhammad ta na ganin da gan-gan ake yaudarar mutane da cewa za a yaki Jahmuriyyar Nijar da sunan an yi wa farar hula juyin mulki.

An ji labari Naja’atu ta ce Tinubu ya san bai cancanci mulki ba saboda haka ya fake da yakar Nijar domin kauda tunanin jama’a daga shari’ar zabe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel