Dalar Amurka Ta Kai N950 a Karon Farko a Najeriya, Tinubu Ya Kafa Mugun Tarihi

Dalar Amurka Ta Kai N950 a Karon Farko a Najeriya, Tinubu Ya Kafa Mugun Tarihi

  • Lamarin Naira sai an hada da addu’a domin kusan kullum darajar kudin ya na karyewa a kasuwa
  • Dalar Amurka ta tashi da fiye da N50 a cikin sa’a 24, hakan ya jawo Naira ta kafa mugun tarihi
  • A yanzu Dala ta na cigaba da kara yin wahalar samu a kasuwar I &E da hannun masu canjin kudi

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Darajar Naira kara fadi kurum ta ke yi a kasuwar canji, inda a yau Alhamis aka ji labari an saida Dalar Amurka a kan N950.

The Cable ta ce N950 da aka saida kudin Amurkan a kasuwar canji ya na nufin Naira ta karye da N53 kusan 5.9% a cikin kwanaki.

A farkon makon nan abin da aka saida $1 bai wuce N897 ba, amma zuwa yanzu labarin ya canza kafin a gama kafa gwamnati.

Kara karanta wannan

Juyin Mulki: Bidiyo Ya Bayyana Yayin da Asari Dokubo Ya Sha Alwashin Yin Kasa-Kasa Da Gwamnatin Sojan Nijar

Dala $1
Dalar Amurka Hoto: Getty Images Wannan hoto kwatance ne
Asali: Getty Images

Bureaux De Change (BDC) da aka fi sani da ‘Yan canji da ke Legas sun bayyana cewa mutane su na neman Dalar Amurka ido rufe.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Masu harkar canjin kudin su na sayen Dala ne kan N935, su kuma sai su saida ta a kan N950, hakan ya ba su damar cin ribar N15.

A kasuwar Agbara a jihar Ogun, ana sayen Dalar ne a N920, sai a saidawa jama’a a N940a sakamkon sabon tsarin da CBN ya kawo.

"Dala tayi wahala yanzu. Farashin kara yin sama yake yi kawai kuma ba mu san dalili ba. Duk da haka mutane na neman kadan da aka samu."

Inji wani Aliyu da ke kasuwancin canji a Abuja.

A kasuwar I & E da masu shigo da kaya su ke sayen kudin kasashen waje, Dalar Amurkan ta tashi da 3.28%, CBN ya na saida ta a kan N782.38/$.

Kara karanta wannan

Aliko Dangote Ya Tafka Asarar Fiye Da Naira Biliyan 480 A Cikin Sa’o’i 24, Arzikinsa Ya Yi Kasa

Kamar yadda jaridar ta kawo rahoto, tun da bankin CBN ya kirkiro kasuwar I & E, ba a taba saida Dala a kan fiye da N800 a tarihinta ba.

Wani ‘dalibin Najeriya da ke karatun jami’a a kasar Indiya, ya fadawa Legit.ng Hausa yadda su ke wahala domin samun kudin kasar wajen.

Za a farfado da tattalin arziki

Kun samu labari daya daga cikin ‘yan kwamitin tattalin arziki da yi wa haraji garambawul budurwa ce mai suna, Orire Agbaje.

Orire Agbaje dalibar ilmin tattalin arziki ce a jami’ar Ibadan da ke aji hudu, ita ce shugabar kungiyar @ui_taxclub da @SEIHUnibadan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel