Ministocin Tinubu: Mutum 5 Da Suka Sha Wahala Kafin a Tantance Su a Majalisa

Ministocin Tinubu: Mutum 5 Da Suka Sha Wahala Kafin a Tantance Su a Majalisa

  • Bola Ahmed Tinubu ya zabi wadanda ya ke so su zama Ministoci, kuma an tantance su a Majalisa
  • Wasu daga cikin mutanen da aka tantance sun yabawa aya zaki da su ka shiga hannun Sanatocin
  • An nemi bijirowa Nasir El-Rufai korafi a kan shi, wasu kuma sun taba yin kalaman da su ka biyo su

Abuja – Mun kawo jeringiyar wasu ‘yan siyasa ko kwararrun a fannoninsu da su ga ta kan su da su ka tsaya gaban Sanatoci da nufin zama ministoci.

Shugaban Majalisa
Shugaban Majalisa ana tantance Ministoci Hoto: SPNigeria
Asali: Twitter

1. Bello Muhammed Goronyo

Da aka zo tantance Bello Muhammed Goronyo, abin da ya jawo magana shi ne yadda ya shiga jami’a ba tare da gagarumar nasara a jarrabawa O’level.

‘Dan siyasar ya kare kan shi, ya fadawa Sanatocin ya na da wasu takardun shaidar dabam da bai kawo masu ba, a karshe aka amince ya rike mukamin.

Kara karanta wannan

Gwamnan CBN Ya Fadi Abin Da Ya Jawo Naira Ta Sunkuya War-Was a Kasuwar Canji

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

2. Minista mai dogon kafa - Joseph Utsev

Abin da ya kusa kawowa Farfesa Joseph Utsev matsala shi ne shekarun haihuwarsa. Injiniyan ya yi ikirarin an haife shi a 1980, abin ya jawo alamar tambaya.

Idan aka dauki wannan lissafi, shekarar shi uku kacal kenan ya fara makarantar firamare a Duniya.

3. Barambarar Bosun Tijjani a Twitter

Tun da Bola Ahmed Tinubu ya aika sunan Bosun Tijjani, aka fara lalubo abubuwan da ya fada game da Najeriya, ‘Yan majalisa, APC da Muhammadu Buhari.

Da Bosun Tijjani ya je majalisa, an dauko masa abubuwan da ya fada a Twitter a shekarun baya, da ya bada hakuri, sai aka yi na'am da a ba shi mukamin.

4. Nasir El-Rufai

Tsohon Gwamna, Nasir El-Rufai ya amsa tambayoyin Sanatoci irinsu Abdulaziz Yari, ya nuna ya za a magance matsalar lantarki idan ya zama Minista.

Kara karanta wannan

Abin Da Ya Jawowa El-Rufai, Danladi Da Okotete Samun Tasgaro a Zama Ministoci

Sanata Sunday Karimi ya bijiro da korafi a kan El-Rufai, amma ba a bada damar kawo batun ba.

5. Festus Keyamo

Tsohon Minista Festus Keyamo (SAN) ya ji babu dadi da ya koma majalisa, bayan gama gabatar da kan shi, sai aka tuna masa abin da ya faru tun 2020.

Lauyan ya taba watsawa ‘yan majalisa kasa a ido da su ka gayyace, dole ya bada hakuri kan hakan.

Binciken jami'an tsaro ya taba Ministoci

Kun ji labari cewa a doka, jami’an tsaro su kan yi bincike a kan mutum, sannan su goyi bayan ya rike mukami ko akasin haka a gwamnatin tarayya.

Malam Nasir El-Rufai, Abubakar Sani Danladi da Stella Okotete su ne wadanda binciken da ake yi bai ba su damar su zama ministoci ba tukuna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel