El-Rufai Ya Daina Sha’awar Zama Ministan Tinubu, Ya Bada Sunan Sabon Madadinsa

El-Rufai Ya Daina Sha’awar Zama Ministan Tinubu, Ya Bada Sunan Sabon Madadinsa

  • Watakila Nasir El-Rufai ba zai shiga cikin ministocin da Bola Tinubu zai yi aiki da su a mulki ba
  • A wani zama da tsohon Gwamnan ya yi da shugaban kasa, ya nuna ya daina sha’awar mukami
  • Hakan ya biyo bayan cikas da El-Rufai ya samu daga jami’an tsaro wajen tantance shi a Majalisa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Wani rahoto da Premium Times ta kadaita da shi, ya bayyana cewa Nasir El-Rufai bai sha’awar zama minista a sabuwar gwamnatin tarayya.

Nasir El-Rufai bai sha’awar yin aiki da Bola Ahmed Tinubu bayan abin da ya faru a wajen tantance wadanda ake so su zama ministoci a kasar nan.

Da aka yi zama da tsohon gwamnan na jihar Kaduna a makon nan, wasu majiyoyi sun shaida cewa ya fadawa Bola Tinubu bai sha’awar rike mukami.

Kara karanta wannan

WAIWAYE: ‘Na Fi So Na Ba Tinubu Gudunmawa Daga Waje’, El-Rufai Ya Magantu Kan Mukamin Minista

El Rufai da Tinubu
Nasir El Rufai da Bola Tinubu Hoto: @Elrufai
Asali: Twitter

Malam El-Rufai ba zai shiga gwamnati ba?

Malam Nasir El-Rufai ya nuna zai bada gudumuwarsa wajen gyara kasa a matsayin mai zaman kan shi, ba tare da ya taka rawar gani a gwamnati ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tsohon ministan ya nunawa shugaba Bola Tinubu cewa ya na bukatar lokaci domin ya maida hankali a kan karatun digir-digir da yake yi a kasar waje.

El-Rufai ya na kokarin kammala digirinsa na PhD a wata jami’a da ke kasar Netherlands a Turai.

Wanda zai canji El-Rufai

Rahoton ya ce idan ana bukatar shawararsa a kan wanda zai iya rike kujerar minista a gwamnatin tarayya, El-Rufai ya bada sunan Jafaru Ibrahim Sani.

Malam Jafaru Ibrahim Sani ya rike matsayin kwamishina a ma’aikatar kananan hukumomi, ilmi da muhalli a lokacin ‘dan siyasar ya na Gwamna.

Idan an gagara shawo kan shi, watakila a dauki Jafaru Sani ko wani dabam daga Kaduna domin a samu wanda zai wakilci jihar a majalisar ministoci.

Kara karanta wannan

Ministocin Tinubu: Mutum 5 Da Suka Sha Wahala Kafin a Tantance Su a Majalisa

Haduwar El-Rufai da Tinubu

Da jin labarin jami’an tsaro ba su kai ga yin na’am da nadin shi a matsayin minista ba, El-Rufai ya na dawowa, ya nemi ya zauna da shugaban Najeriya.

A lokacin da labarin ya fito, rahoton ya ce Malam ya iso Najeriya daga Landan kenan.

A wajen zaman ne Bola Tinubu ya fada masa SSS ta aiko korafi game da shi, kuma ana bukatar a duba rahoton, a nan ya nuna bai bukatar wani mukami.

Yadda Tinubu ya nemi alfarmar El-Rufai

Kwanaki kun ji labari an gano bidiyo a Twitter inda Bola Tinubu da kan shi ya ke rokon Nasir El-Rufai ya yi aiki da gwamnatinsa idan an ci zabe.

A lokacin kamfe, Malam El-Rufai ya nuna cewa shekaru sun ci masa, saboda haka bai bukatar ya rike kujerar da ya bari tun a Mayun shekarar 2007.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng