Muhammad Malumfashi
19978 articles published since 15 Yun 2016
19978 articles published since 15 Yun 2016
Muhammadu Buhari ya kewaye kan shi da barayin gwamnati a mulkinsa. Irinsu Ali Ndume su na zargin akwai wasu miyagu da aka yi a gwamnatin 2015 zuwa 2023.
Ginin da ke dauke da ofishin shugabanni da jami’an jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ya kama da wuta a ranar Juma’ar nan, amma abin ya zo da sauki.
Shehin Malami, Adam Abdallah Hotoro ya yi magana kan zaben Kano da shari’ar da ake yi, ya ce zaman lafiya da adalci shine a bar mutane da zabin su a jihar Kano.
Mafi karancin albashi a yau N30, 000 ne, zuwa Maris babu wanda za a biya wannan kudi.Gwamnati ta ce nan da 'yan watanni kadan sabon tsarin albashi zai soma aiki.
Lauyan NNPP ya gabatar da korafin da ake sa rai za su sa Abba Kabir Yusuf ya tsira a kotun koli. Wole Olanipekun, SAN ya nunawa kotu yadda aka cinyewa NNPP kuri’u.
Wasu `yan majalisar tarayya su na zargin cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya yaudare su inda suka ce ya mika musu kundin kudurin kasafin kudin 2024 na bogi.
Bola Tinubu ya na so a rage yawan mutanen da ke garkame a gidajen gyaran hali. Za a tanadi N580m domin a fanshi mutane fiye da 4000 da aka daure a kurkuku.
Majalisar dattawa ta ce bincikenta ya nuna mata an karkatar da kudin tallafin da bankin CBN ya ba kamfanoni. Biliyoyin da CBN ya ba kamfanonin mai sun bi iska.
Tukur Sani Jangebe ya yi wa Bello Matawalle addu’ar samun nasara a zaben gwamna da za ayi a wasu garuruwan Zamfara wanda hakan ya fusata Gwamna mai-ci, Dauda Lawal.
Muhammad Malumfashi
Samu kari