Tinubu Ya Warewa Buhari, Osinbajo da Jonathan Naira Biliyan 13 a Kasafin Kudin 2024

Tinubu Ya Warewa Buhari, Osinbajo da Jonathan Naira Biliyan 13 a Kasafin Kudin 2024

  • Tsofaffin shugabannin kasa na mulkin farar hula da sojoji su na da kaso a kasafin kudin shekarar 2024
  • Gwamnatin Bola Tinubu za ta batar da biliyoyi a kan shugabannin kasar da su ka yi mulki da mataimakansu
  • Jami’an da su ka kai matsayin shugabannin hukumomi da ma’aikatun Gwamnatin Tarayya za su samu N10bn

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Gwamnatin tarayya ta ware N13,805,814,220 domin dawainiyar tsofaffin shugabanni da mataimakansu da aka yi a kasar nan.

Punch ta ce shugabannin kasa da mataimakansu da aka yi a lokacin mulkin soja har zuwa mulkin farar hula za su amfana da wadannan kudi.

Bola Tinubu
Bola Tinubu ya yi ksasafin kudin 2024 Hoto: Ajuri Ngalele
Asali: Facebook

Sauran wadanda za a biya alawus daga kason su ne tsofaffin shugabannin ma’aikata da manyan sakatarorin gwamnatin tarayya masu ritaya.

Kara karanta wannan

Fankon kundin kasafin kudi Tinubu ya gabatarwa yan majalisa? Daga karshe gaskiya ta bayyana

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jami’an da su ka rike shugabancin hukumomi, cibiyoyi da ma’aikatun gwamnatin tarayya za su samu kasonsu a cikin kasafin kudin na 2024.

Za a biya Obasanjo, Jonathan da Buhari a kasafn kudi

A shugabannin fararen hula gwamnatin tarayya za ta biya alawus ga Olusegun Obasanjo, Dr. Goodluck Jonathan da kuma Muhammadu Buhari.

Haka akwai Alhaji Atiku Abubakar, Arch. Namadi Sambo da Farfesa Yemi Osinbajo.

Tsofaffin shugabannin soji da aka ware kudin da su sun kunshi; Janar Yakubu Gowon, Janar Abdusalami Abubakar da Janar Ibrahim Babangida.

Air Commodore Ebitu Ukiwe (retd.). wanda ya yi wa Babangida mataimaki ya na cikinsu. Irinsu Janar Oladipo Diya da Tunde Idiagbon duk sun rasu.

Karin albashi a kasafin kudin 2024

Shugabannin kasa za su tashi da N2.3bn sai N11.5bn za su tafi ga tsofaffin shugabannin hukumomi da manyan sakatarori da su ka yi ritaya.

Kara karanta wannan

Kakakin Majalisar Wakilai ya karanto sunayen sabbin shugabannin kwamitoci 27 da mataimaka

Daily Post ta ce an ware N1tr domin a iya sallamar ma’aikatan da aka yi wa karin albashi.

Yadda ake biyan tsofaffin shugabanni

Ba wannan ne karon farko da aka biya tsofaffin shugabanni, a kan yi masu tanadin alawus na musamman da zai iya kula da su bayan barin ofis.

Da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi kasafin N16tr a 2022, tsofaffin Shugabanni da Ma’aikatan Gwamnati sun lamushe Biliyoyin kudi a shekarar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng