An Yanka ta Tashi a NNPC, Tsohon Sanata Ya Kalubalanci Nade Naden Mukaman Tinubu

An Yanka ta Tashi a NNPC, Tsohon Sanata Ya Kalubalanci Nade Naden Mukaman Tinubu

  • Ifeanyi Araraume zai ja da Mai girma Bola Ahmed Tinubu a kan mukaman da ya nada a kamfanin NNPCL kwanan nan
  • ‘Dan siyasar ya ce akwai shari’a da aka yi a kotun tarayya wanda ta haramta nadin wasu shugabanni a kamfanin man
  • Sanata Ifeanyi Araraume ya bukaci shugaba Tinubu ya janye nadin da ya yi, ya bar dokar kasa da shari’a su yi aikinsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja – Sanata Ifeanyi Araraume ya bukaci Bola Ahmed Tinubu ya soke nade-naden da ya yi a kamfanin mai na kasa watau NNPCL.

Kamar yadda labari ya zo a The Cable, Ifeanyi Araraume wanda ya taba wakiltar Arewacin Imo a majalisar dattawa ya ce an saba doka.

Kara karanta wannan

Bai san ana yi ba, Sanatan APC ya fadi babban kuskuren Buhari a shekaru 8

Tinubu
Shugaban Najeriya ya nada shugabannin NNPCL Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Mukaman da aka nada a NNPCL

‘Dan siyasar ya na ganin cewa nadin shugabannin kamfanin NNPC ya ci karo da dokar kasa, ya bukaci a kori wadanda aka nadan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A makon jiya ne Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya amince Mele Kolo Kyari ya cigaba da rike kujerar da yake kai na shugaban NNPCL.

Bayan haka an nada Pius Akinyelure ya jagoranci majalisar da ke kula da aikin NNPCL.

NNPCL: Lauyan Ifeanyi Araraume ga Bola Tinubu

Ifeanyi Araraume ya soki lamarin inda ya yi magana ta bakin lauyansa, ya na mai cewa an yi nadin da ya ci karo da umarnin kotun tarayya.

A jawabin da Ogwu Onoja ya fitar, an zargi gwamnatin Bola Tinubu da yi wa kotu rashin da’a wajen nadawa NNPC sababbin shugabanni.

Ogwu Onoja yake cewa sun yi mamakin yadda shugaban kasa zai saba doka, ya yi watsi da hukuncin da Mai shari’a Inyang Ekwo ya yi.

Kara karanta wannan

Ministan Jonathan Ya Shaidawa Kotu Yadda Aka ba Tsohon Gwamna N1.2bn a Lashe Zabe

Premium Times ta ce Lauyan ya ce bayan gwamnati mai-ci ta daukaka kara a kan shari’ar Alkali Inyang Ekwo, ba ta jira hukunci ba.

Tinubu ya sabawa doka a nada shugabannin NNPCL?

"Abin takaici, wannan aiki da Mai girma shugaban kasa ya yi, ya nuna rashin bin doka, sannan fito na fito ne da bangaren shari’a.
Tun da hukuncin da aka yi na nan, shakka babu nadin sababbin shugabannin NNPC ya saba doka, ba daidai ba ne, kuma batacce ne."

- Ogwu Onoja

Rikicin Ararume da Buhari a NNPCL

Ana da labari Ifeanyi Ararume bai wuce ‘yan kwanaki a ofis ba, aka sanar da shi cewa an fatattake shi daga mukamin da aka ba shi a NNPCL.

Tsohon 'dan majalisar ya kalubalanci Muhammadu Buhari a lokacin, kuma kotun da ke zama a Abuja ta ce a maida shi, a biya shi duk hakkokinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel