Addu’ar Neman Nasarar APC a Zaben Gwamnan Zamfara Ta Jawo Malami Ya Shiga Uku

Addu’ar Neman Nasarar APC a Zaben Gwamnan Zamfara Ta Jawo Malami Ya Shiga Uku

  • Tukur Sani Jangebe ya yi wa Bello Matawalle addu’ar samun nasara a zaben gwamna da za ayi a wasu garuruwan Zamfara
  • Malamin ya na zargin cewa a kan haka ne gwamnatin Dauda Lawal ta kitsa yadda za a kore shi daga limancin masallacin Juma’a
  • Sheikh Jangebe ya hakura da kujerarsa da ya hangi take-taken da ake yi, yanzu haka ana wasan buya da shi a jihar Zamfara

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Zamfara - A watan Nuwamban da ta gabata, Tukur Sani Jangebe ya shirya addu’a ta musamman domin ganin nasarar APC a zaben jihar Zamfara.

Za a gudanar da zabe a kananan hukumomi uku a sakamakon hukuncin kotu, Daily Trust ta ce Sheikh Tukur Sani Jangebe ya rokawa APC nasara.

Kara karanta wannan

Malamin musulunci ya fadi abin da zai faru idan aka ‘karbe’ kujerar gwamnan Kano

Malamin ya yi addu’a domin Bello Muhammad Matawalle ya samu nasara a zaben da za ayi, an yi addu’o’in ne a gidan tsohon gwamna a Muradun.

Tukur Jengebe
Dauda Lawal da Tukur Jengebe Hoto: Sheikh Dr. Imam Muhammadu Tukur Sani Jangebe da Dauda Lawal
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tun ba yau ba, Sheikh Tukur Jengebe wanda yanzu haka ana zargin yana wasan buya da hukuma ya saba yi wa ‘yan siyasa da masu mulki addu’o’i.

Addu'o'in Sheikh Tukur Sani Jangebe

Rahoton ya ce a baya ya yi wa Ahmad Yariman Bakura, Abdulaziz Abubakar Yari, Muhammad Bello Matawalle har da Dr Dauda Lawal addu’a.

A lokacin da Kanal J. B. Ibrahim (rtd) ya je gidan yari, ya yi masa addu’a, haka zalika lokacin da aka tsare Alhaji Ibrahim Ruwan Dorawa a Saudi.

Sheikh Tukur Jangebe a mulkin PDP

Sheikh Jangebe ya taba yi wa Dauda Lawal addu’a duk da ya na Kwamishina a gwamnatin Matawalle, amma wannan karon abin ya canza.

Kara karanta wannan

Alkalan da suka yi kuskure a shari’ar zaben Kano za su yabawa aya zaki a Majalisar Shari’a

Gwamnatin PDP ba ta ji dadin yadda malamin ya fito ya na rokon Allah SWT ya ba Matawalle galaba a kan Dauda Lawal a zaben gwamna ba.

Ana zargin hakan ne dalilin da malamin ya rasa kujerarsa ta limamin Juma’a ta hanyar hada kai da kwamitin masallacin domin a tsige shi.

Kamar yadda ya fada, da jin shirin da ake yi domin kunyata, shi kuma Sheikh Jengebe sai ya rubuta wasika, ya ce ya bar limanci a Gusau.

An hana yi wa APC addu'a a Zamfara

Sheikh Jangebe ya ce a al’adarsa, ya kan yi wa duk wani ‘dan siyasa addu’a muddin ya na takara tun daga shi Bello Matawalle har Dauda Lawal.

Zuwa yanzu gwamnatin Dauda ta haramta yi wa APC ko Bola Tinubu addu’a a Zamfara.

Malamin ya tabbatar da cewa ya boye a Gusau da ya fuskanci ya na fuskantar barazana, ya ce ba zai dawo ba har sai abubuwa sun lafa tukun.

Kara karanta wannan

Abba Gida Gida: Mata sun barke da zanga-zanga a kan tsige Gwamnan Kano a Kotu

Ana da labari Sheikh Mohammed bn Othman ya yi huduba, inda ya ce an fito da tsarin Agile ne domin a gurbata tarbiyar matan da ke Arewa.

Shugabar cibiyar CGE, Habibah Mohammed ta fayyace yadda Agile ta ke aiki a Najeriya, ta nuna tsarin bai da alaka da gurbata tarbiyyar yara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel