Nasarawa da Kuros Ribas Sun Tashi da Cinyoyi da Aka Rabawa Jihohi Biliyoyin Kudi

Nasarawa da Kuros Ribas Sun Tashi da Cinyoyi da Aka Rabawa Jihohi Biliyoyin Kudi

  • Bankin duniya ya ba NG-CARES gudumuwa domin tallafawa wadanda annobar COVID-19 ta durkusa hanyar neman kudinsu
  • Gwamnatin tarayya ta rabawa jihohin Najeriya da birnin tarayya Abuja tallafin Naira biliyan 135 a karkashin tsarin NG-CARES
  • Dr. Abdulkarim Obaje ya ce akwai ka’idar da aka bi wajen bada tallafin, wannan ne ya sa jihar Nasarawa ta zo ta farko a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Gwamnatin tarayya ta raba N135.4bn ga jihohi da kuma birnin Abuja domin farfado da tattalin arziki bayan annobar COVID-19.

Rahoton da aka samu daga Punch ya nuna an raba kudin ne bayan lura da yadda jihohi su ka yi kokarin tada komadan tattalin arzikinsu.

Bola Ahmed Tinubu
Gwamnati ta rabawa jihohi tallafi Hoto: Asiwaju Bola Tinubu
Asali: Twitter

NG-CARES ya ba jihohi tallafin N135bn

Kara karanta wannan

Shin Tinubu ne? Atiku ya bayyana wanda ya siyarwa hannun jarinsa na $100m a kamfanin Intels

Shugaban tsarin NG-CARES, Dr. Abdulkarim Obaje, ya sanar da haka a wani jawabi da ya fitar ta bakin Mr. Suleiman Odapu a ranar Lahadi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Suleiman Odapu shi ne jami’in yada labarai da sanarwa a karkashin tsarin na NG-CARES.

Bankin duniya ya tallafawa tsarin NG-CARES da $750m da nufin taimakawa kananan ‘yan kasuwa da manoman da COVID-19 ta taba.

Dr. Abdulkarim Obaje ya ce kudin da aka rabawa jihohin ya danganta ne da kokarin da su ka yi wajen taimakawa wadanda annobar ta shafa.

Dr. Obaje ya bayyana jihohin da su ka fi yin kokari da kuma adadin kudin da aka ba su.

Yadda aka yi rabon kudin tallafin

Jaridar ta ce jihar Nasarawa ce a kan gaba da ta samu N13.6bn, sai Kuros Riba mai N10.9bn sai kuma jihar Zamfara wanda ta tashi da N10.2bn.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu Ta Tsaida Lokacin Fara Biyan Sabon Tsarin Albashin Ma’aikata

Wadannan jihohi uku sun tashi da 34,873,631,583.62 daga cikin tallafin biliyoyin da aka raba, ma’ana su kadai sun samu fiye da 25% na kason.

Kokarin Gwamnatin Tinubu a Najeriya

Jawabin ya kara da cewa wannan wata nasara ce da aka samu a gwamnatin Bola Tinubu.

Sabon shugaban na Najeriya ya ci burin rage jarabar talaucin da ake fama da shi a Najeriya, wannan ya na cikin kudirorin gwamnatinsa.

An fara biyan giratuti a jihar Kano

Sabon Gwamnan jihar Kano ya tabbatarwa tsofaffin ma’aikata shi mai kaunarsu ne inda aka ji zai kashe N6bn wajen biyan giratutinsu.

Bayan shekaru 'yan fansho su na jiran hakkokinsu, Abba Kabir Yusuf ya share masu hawaye a Kano kamar yadda ya dauki masu alkawari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng