Gwamnatin Tarayya Za Ta Biya N585m a Shiga Sallamar Wadanda Aka Daure a Kurkuku

Gwamnatin Tarayya Za Ta Biya N585m a Shiga Sallamar Wadanda Aka Daure a Kurkuku

  • Gwamnatin tarayya ta kudiri niyyar rage cinkoson da ake da shi a mafi yawan gidajen yari da ake da su a Najeriya
  • Ministan harkokin cikin gida ya ce za a tanadi N580m domin a fanshi mutane fiye da 4000 da aka daure su a kurkuku
  • Dr. Olubunmi Tunji-Ojo ya nuna babu ta yadda za a ji dadin zama har wadanda ke gidajen gyaran hali su shiryu a haka

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Gwamnatin tarayya za ta tara N585m da za a biya a matsayin tarar wadanda ke daure a gidajen gyaran hali da ke fadin Najeriya.

Ministan harkokin cikin gida, Dr. Olubunmi Tunji-Ojo ya shaida wannan a lokacin da aka saki wasu da ke daure, Punch ta kawo rahoton nan.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu Ta Tsaida Lokacin Fara Biyan Sabon Tsarin Albashin Ma’aikata

Gidan yari
Kurkuku a kasar waje Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

A ranar Alhamis, gwamnatin tarayya ta fito da wasu mutane daga gidajen gyaran hali da ke Kano bayan an biya tarar da kotu ta yanke masu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutum 4,000 tara ta kai kurkuku

Darektan ma’aikatar cikin gida, Dr Anayo Romanus-Nzekwe ya wakilci Mai girma Minista Dr. Tunji-Ojo a wajen fito da ‘yan gidan kason a Kano.

Sabon ministan ya ce mutane sama da 4, 000 ke garkame a gidajen gyaran hali saboda sun gagara biyan tara ko kudin da Alkali ya yanke masu.

Tunji-Ojo ya yi alkawari gwamnatin tarayya za ta biya kudin da ake bin mutanen da ke tsare, adadin tara da hakkokin wuyansu ya zarcw N500m.

An fito da mutane a kurkuku a Kano

Wani rahoton ya ce mutane sama da 150 aka fito da su daga babban gidan gyaran hali na Janguza da ke garin Kano a cikin ‘yan kwanakin nan.

Kara karanta wannan

"Cin zabe sai an hada da rauhanai" Shehu Sani ya yi wa Doguwa martani

Romanus-Nzekwe yake cewa wadannan mutane 150 su na cikin ‘yan gidajen yari 4, 068 da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta ke nemawa ‘yanci.

Gwamnatin tarayya ta na so a rage cunkoso a gidajen gyaran hali kuma su zama inda mutum zai iya rayuwa domin gyaruwa da shiryuwa.

Zuwa yanzu mutane 141 aka fitar daga gidajen yari da ke jihar Gombe wanda daga ciki akwai da-dama da ke gidan kurkuku na garin Billari.

Majalisa za ta kai kara a EFCC?

Mu na da rahoto cewa kwamitin majalisar dattawa ya ce bincike ya nuna mata an karkatar da kudin tallafin da bankin CBN ya ba kamfanoni.

CBN ya bada aron kudi ga NIPCO Plc, Hyde Energy Ltd, Lee Engineering & Construction, sai gwamnatin jihar Delta da matatar Dangote.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng