Abba Gida Gida: Yadda ‘Yan Fansho Suka Mutu Saboda Zalunci Lokacin Mulkin APC

Abba Gida Gida: Yadda ‘Yan Fansho Suka Mutu Saboda Zalunci Lokacin Mulkin APC

  • Abba Kabir Yusuf ya zargi gwamnatin da ta shude a jihar Kano da zaluntar tsofaffin ma’aikatan gwamnati
  • Gwamnan jihar Kano ya bada labarin yadda wani dattijo ya rasu a sakamakon hana shi kudin sallama daga aiki
  • Mai girma Abba Kabir Yusuf ya warewa tsofaffin ma’aikata N6bn da za a biya giratutin da aka dade ana sauraro

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya bada labarin yadda aka zalunci tsofaffin ma’aikata, aka hana su hakkokinsu bayan ritaya.

Abba Kabir Yusuf ya yi wannan bayani wajen kaddamar da biyan giratutin ma’aikatan da su ka yi ritaya a Kano a cewar Premium Times.

Abba Gida Gida
Gwamnan Kano ya biya giratuti Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Wahalar 'yan fansho a Kano - Abba

Kara karanta wannan

Ma'aikacin Karamar Hukuma Ya Fadi Matacce a Ofis, Bayanai Sun Fito

Gwamnan yake cewa akwai wani tsohon ma’aikaci da ya mutu bayan bada cin hanci ga jami’in gwamnatin jiha saboda ya samu hakkinsa ya fito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda gwamnan ya bada labari, wannan dattijon ya na karbar fansho, yana neman kudi ido rufe domin ya aurar da diyarsa a gidan mijinta.

Jami’in gwamnatin da ya nemi cin hanci ya fada masa idan har yana son kudinsa su fito da wuri, dole ya yafe daya bisa ukun kudin giratutin na sa.

An rahoto Abba Gida Gida ya na cewa ‘dan fanshon ya yi ta daga auren ‘yarsa saboda rashin kudi domin gwamnatin baya ta ki biyan giratutin jama’a.

Abba ya ce tsofaffin ma'aikata sun mutu

A karshe wannan Bawan Allah ya hakura cewa zai bada kason da ake bukata daga kudin sallamar, amma duk da ya yi hakan, hakkin na sa bai fito ba.

Kara karanta wannan

Kano: Gwamna Abba Kabir ya sanya yan fansho kuka yayin da ya cika musu alkwarin da ya dauka, ya koka

Gwamnan ya ce a karshe tsohon ya gamu da hawan jinin da ya yi sanadiyyar mutuwarsa.

An biya giratutin ma'aikata a Kano

Da gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta sallami ma’aikata, aka warewa tsofaffin ma’aikata N6bn, marigayin ya na cikin wadanda aka sallami iyalinsa.

Abba ya na ganin laifin gwamnatin da ta wuce wajen rashin biyan ma’aikata kudinsu, yake cewa gwamnatin NNPP na kaunar al’ummar jihar Kano.

“Mu na so duniya ta sani cewa mu masoyanku ne, kuma da yardar Allah, azzalumai ba za su sake samun gurbi a jihar Kano ba.”

- Abba Kabir Yusuf

Sanata ya soki shirin tsige Abba

Rahoto ya zo cewa Abdulrahman Kawu Sumaila ya yi Allah wadai da hukuncin shari’ar Gwamna Abba Kabir Yusuf da APC a kan zaben 2023.

Sanatan Kano ta kudu ya ce ana shirin tsige Abba Kabir Yusuf, a mika mulki ga wanda ya san bai ci zabe ba inda ya yi kira abin rashin adalci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel